Taruka biyu na majalisar wakilan jama’ar Sin wato NPC da na majalisar ba da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar wato CPPCC, wani muhimmin dandali ne ga kasashen duniya wajen duba demokuradiyya irin ta kasar Sin. A gun bikin rufe taron NPC da aka gudanar jiya Laraba, wakilan da suka halarci taron sun zartas da kuduri kan dokar NPC da tarukan wakilan wurare daban-daban, abun da ya zama wani sabon mataki na duba salon demokuradiyyar Sin.
A nan kasar Sin, wakilan NPC su kasance mahadar jam’iyyar JKS da jama’a, inda suke aiwatar da hakkinsu bisa doka da gabatar da ra’ayoyi da bukatu na jama’a ga gwamnatin kasar. Burin gyara dokar wakilan NPC shi ne tabbatar da hakkin jama’a a bangaren demokuradiyya, abin da kuma ya bai wa tsarin zamanantar da al’ummar Sinawa tabbaci irin na doka da manufa.
- Kasar Sin Ta Harba Taurarin Dan’Adam 18 Daga Cibiyar Harba Kumbo Ta Kasuwanci Ta Hainan
- Mutum 1,010 Sun Mutu Sakamakon Hare-hare A Watan Fabrairu – Rahoto
Kazalika, ma’anar demokuradiyya a nan kasar Sin ita ce sauraron ra’ayoyin jama’a da amsa su don taimaka musu wajen daidaita matsalolin da suke fuskanta. Matakin da ya bayyana ruhin tsarin zamanantar da al’ummar, wato mai da muradun jama’a a gaban komai.
Sin ta yi iyakacin kokarin kyautata tsarin demokuradiyyarta don tabbatar da cewa, an aiwatar da manufofi kan lokaci, da gaggauta bunkasar ingantattun tattalin arziki da kyautatuwar zaman rayuwar jama’a. A shekarun baya-bayan nan, Sinawa na tinkarar matsaloli da kuma kokarin kirkire-kirkire kafada da kafada, tare da nuna karfin zuciya wajen yin kokari tare ta yadda za su shaida hakkinsu a bangaren demokuradiyya.
Ana raya demokuradiyya a dukkan fannoni yayin da ake zamamantar da al’ummar Sinawa, inda hakan ke kara sanya su taimaka wa juna da tabbatar da ci gaban juna. Ba tabbatar da aikin zamamantar da al’ummar Sinawa mai dorewa kawai ake yi ba, har ma ana inganta demokuradiyya irin ta Sin da habaka ma’anar wayewar kan dan Adam. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp