Dakarun sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kubutar da wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su a Zamfara.
Rundunar sojin Nijeriya ta sanar da hakan ne a shafinta na X wanda aka fi sani da Twitter a baya, inda ta ce, sojojin da aka tura a karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara sun amsa kiran gaggawa kan wani hari da ‘yan ta’adda suka kai wa wasu manoma a hanyar Gidan Shaho.
- Badakalar Fiye Da Biliyan 8: EFCC Ta Cafke Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika
- Mayakan Boko Haram 2 Sun Mika Wuya Ga Sojoji
Sanarwar ta ce, ‘yan ta’addan da suka ga sojoji Sun tsere inda suka bar wadanda suka yi garkuwa da su.
Rundunar sojin ta kuma bayyana cewa, wadanda suka samu raunukan harbin bindiga daga cikin wadanda aka ceto, an kwashe su cikin gaggawa zuwa babban asibitin jihar domin kula da lafiyarsu.