Shugabannin al’umma a Kananan Hukumomin Jibiya, Batsari da Safana na Jihar Katsina, sun cimma yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindigar da ke addabar kauyukansu.
Mazauna yankin sun ce, an yi zaman sulhun a baya-bayan nan tsakanin Shugabannin Karamar Hukumar Jibiya da ‘yan ta’adda a ranar Juma’a 28 ga watan Fabrairu, biyo bayan irin wannan yarjejeniyoyin da aka yi a Kananan Hukumomin Batsari da Safana, wadanda suka sha fama da hare-hare babu kakkautawa saboda kusancinsu da Dajin Rugga.
- Sin Ba Za Ta Taba Amincewa Da Ayyukan ’Yan Aware Ba
- NPA Za Ta Yunkuro Don Zamanantar Da Ayyukan Tashoshin Jiragen Ruwan Nijeriya – Dantsoho
Har ila yau, kamar yadda suka bayyana; tattaunawar ta samu halartar wakilan sojoji, jami’an tsaron farin kaya (DSS), ‘yansanda, jami’an sa ido na al’umma, ‘yan banga, sarakunan gargajiya da jami’an kananan hukumomi.
Kazalika, an bayyana cewa; wani sanannen shugaban ‘yan bindiga a yankin, Audu Lankai ne ya kaddamar da yarjejeniyar, inda ya nuna takaicinsa kan yadda rikicin ya dade ana yin sa.
Wata majiya mai tushe a Jibiya ta ce, “Babu hannun gwamanatin jihar kai tsaye a sulhun, domin kuwa gwamnan ya sha nanata cewa; ba zai tattauna da ‘yan bindiga ba, matukar ba su mika wuya sakamakon matsin lamba ba.”
“Amma a wannan karon, shugabannin al’ummarmu; sun gana da daya daga cikin manyan jami’an gwamnati, sannan sun ba mu goyon bayansu, bisa la’akari da halin da muke ciki.
Shugaban ‘yan bindigar Audu Lankai ne ya bukaci zaman wannan sulhu tare da bayyana cewa; ya gaji da wadannan tashe-tashen hankula da suke faruwa.
“Ya tuntubi daya daga cikin shugabanninmu, bayan tattaunawa mai tsawo, mun kuma amince da haduwa ranar Juma’a. Kazalika, mun amince da ci gaba da tattaunar zaman lafiya bayan Sallah, idan dukkanin bangarorin biyu suka mutunta sharuddan yarjejeniyar.”
Sharuddan da al’ummar Jibiya suka gindaya, sun hada da dakatar da hare-haren da ake kai wa matafiya a kan titin Jibiya zuwa Katsina, Batsari zuwa Batsari da kuma Jibia zuwa Gurbi da kuma kawo karshen hare-haren da ake kai wa kauyuka da garkuwa da mutane, barin manoma da mazauna yankunansu ci gaba da ayyukansu da sakin wadanda aka kama da kuma ajiye makamai.
Ya kara da cewa, ya zuwa yanzu an kubutar da mutum 11 da aka yi garkuwa da su, sannan ‘yan bindigar sun mika makamai biyu.
Majiyar ta kuma ce, ‘yan bindigar sun bukaci a bai wa ‘yan ta’addar damar shiga cikin al’umma, ba tare da wata barazana ga rayuwarsu ba, saboda bukatar kare kai daga kungiyoyin da ke gaba da juna da kuma wadanda ba ‘yan ta’adda ba.
A cikin wani faifan bidiyo, wani dan bindiga mai suna Bala Wuta, ya yi jawabi a makarantar firamare ta Kwari, inda ya koka da irin asarar da aka samu daga bangarorin biyu.
Ya bukaci gwamnati ta samar da ababen more rayuwa da suka hada da makarantu, wuraren ruwan sha da magunguna ga makiyaya, domin samun fahimtar juna.
Wani daga cikin shugabannin al’umma a Jibiya da bukaci a sake sunansa, ya tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiyar, inda ya ce; “Hatta Annabi Muhammad SAW, ya shiga yarjejeniyar zaman lafiya, ma’ana wannan wani abu ne da Allah ya yarda da shi, domin kuwa; babu wata fa’ida a cikin rikici, idan bangarorin biyu na son kawo karshensa.
Zaman Lafiya Ya Fi Komai Dadi- Mazauna Kauyukan
Mazauna kauyukan da al’amarin ya shafa, sun bayyana jin dadinsu, inda suka bayyana cewa; shirin samar da zaman lafiyar da al’umma ke yi ya fara nuna kyakkyawan sakamako.
Haka zalika, sun bayyana cewa; yankunan da ake gani sun fi hatsarin ziyarta, sannu a hankali ana samun dawowar zaman lafiya na rayuwar yau da kullum.
Malam Yahuza Aliyu, Mataimakin Hakimin Kauyen Wagini a Karamar Hukumar Batsari, ya tuna da yadda aka yi watsi da kauyen da ke dauke dumbin mutane, kuma wannan hare-hare na ‘yan ta’adda ke faruwa a cikinsa.
“Na tuna da wani mummunan al’amari da ya faru ranar Talata, inda mahara suka kai farmaki kauyenmu da misalign karfe hudu na yamma, inda suka yi ta faman harbe-harbe babu kakkautawa tare da tilastawa mazauna garin yin hijira. A wannan rana, wasu mata sun haihu yayin da suke gudu, don tseratar da rayuwarsu, wasu kuma suka yi bari.
Kazalika, haka yara suka rika gudu babu takalmi a kafarsu zuwa garin Batsari, don neman mafaka”, in ji shi.
Aliyu ya kara da cewa, an yi garkuwa da mutanen kauyen da dama, domin samun kudin fansa, yayin da wasu kuma suka rasa rayukansu a hare-haren.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp