A tsakiyar makon nan ne mahukuntan kasar Sin suka mikawa gwamnatin Zimbabwe tallafin gaggawa na kayan abinci, wadanda za a rabawa rukunin mabukata a kasar, wadanda suka hada da mutane masu bukata ta musamman da sauran masu rauni.
Ko shakka babu, wannan tallafi da ya kushi tan 1,000 na shinkafa, da tan 1,000 na alkama, zai yi matukar agazawa masu rauni dake Zimbabwe ta fannin samun isasshiyar cimaka, wanda hakan manufa ce ta bai daya tsakanin Sin da Zimbabwe a bangaren wadatar da al’ummun su da abinci.
Kaza lika, masharhanta na ganin tallafi na Sin a matsayin shaida dake tabbatar da karkon kawancen gargajiya dake tsakanin kasashen biyu.
Ba dai wannan ne karon farko da Zimbabwe, da ma karin wasu kasashen Afirka da dama ke karbar makamancin wannan tallafi daga bangaren kasar Sin ba, wanda hakan ke nuni da cewa, yayin Sin ke samun karin bunkasar tattalin arziki da wadata, a hannu guda ba ta manta da ’yan uwan ta kasashe masu tasowa dake cikin yanayi na bukata ba.
Tuni dai mahukuntan Sin suka cika alkawura masu yawa da suka dauka na bunkasa hadin gwiwa da kasashen Afirka, ciki har da kasar Zimbabwe, kasar da ba ya ga irin wadannan tallafin gaggawa da ta samu daga Sin har karo 10 tsakanin shekarar 2002 zuwa yanzu, ta kuma ci gajiyar agajin bunkasa tattalin arziki, da raya ababen more rayuwa, irin su haka rijiyoyin birtsatsai a yankunan karkararta, da kafa cibiyar gwajin dabarun noma, da madatsun ruwa, da filayen noman rani, da sauran shirye-shiryen hadin gwiwar raya noma da Sin din ke jagoranta. Har ila yau, Zimbabwe ta mori shirye-shiryen tallafawa fannin kiwon lafiya, da ilimi da bunkasa zamantakewar al’umma.
A daya bangaren kuma, kasar Sin tana ci gaba da dora muhimmanci ga tallafawa Zimbabwe da dabarun inganta noma, ta hanyar samar mata da na’urorin aiki na zamani, da bunkasa kwarewa da zuba jari.
La’akari da wannan, da ma sauran fannonin raya ci gaba da Zimbabwe ke mora daga Sin, ya sa mahukuntan kasar ke jinjinawa Sin, tare da kara amincewa da ita a matsayin kawa ta hakika ga ita kanta Zimbabwe din da ma sauran kasashen nahiyar Afirka. (Saminu Alhassan)