Rahoton da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya ta fitar a 2019 ya bayyana cewa Nijeriya ta na asarar kimanin fili mai fadin murabba’in kadada 350,000 a duk shekara, sakamakon yadda hamada ke ci gaba da mamayewar yankuna, wanda hakan ya na faruwa ne ta musababbin sauyin yanayi, mai alaka da ayyukan yau da kullum da Dan Adam masu jawo dumamar yanayi.
A nata bangaren, a wani sabon binciken da Hukumar Agora Policy ta gudanar a wannan shekara (2023), ta bayyana cewa, Nijeriya zata iya yin hasarar Dalar Amurka kimanin biliyan 460 sakamakon sauyin yanayin da duniya ke fuskanta, nan da shekarar 2050 mai zuwa, matukar ba ta dauki ingantattun matakan kan-da-garki ba.
- Akidar Siyasar Malam Aminu Kano Da Ta ‘Yan Siyasar Yanzu A Mizani –Farfesa Habu
- Sojojin Ruwan Kasar Sin Sun Shafe Shekaru 15 Suna Aikin Tabbatar Da Tsaro A Mashigin Tekun Aden Da Gabar Tekun Somaliya
Jihar Yobe ta na daya daga cikin Nijeriya masu fuskantar matsalolin gurgusowar hamada mai alaka da sauyin yanayi, al’amarin da yake da alaka da sha’anin tsarin tattalin arziki, zamantakewa da al’adu, wanda ya dace a samu sauyin da za su taimaka wajen rage dumamar yanayin da canjinsa. Haka kuma, sakamakon tasirin sauyin yanayin ya na shafar yankuna da al’ummar jihar kai-tsaye, wanda yake zama babbar barazana ga ci gaba da yanayin rayuwar mazauna yankunan.
Bugu da kari kuma, yankunan kananan hukumomin Yunusari, Yusufari, Geidam, Bade, Karasuwa, Machina, Bursari, da Tarmuwa a jihar Yobe, su na daga cikin sassan jihar wadanda suke dandana kudarsu a hannun sauyin yanayin, kuma babbar barazana ga mazauna yankunan.
LEADERSHIP Hausa ta jiyo ta bakin Mallam Baba Alkali, Sakataren karamar hukumar Yusufari, a jihar Yobe, ya bayyana cewa sakamakon sauyin yanayin, yankunansu na fuskantar karancin ruwan sama, sabanin shekarun baya, wanda ya jawo tankardar noma da abinci ga al’ummar yankin.
A nashi bangaren, Lawanin kauyen Gremadi, Alhaji Maidala Zanna, ya ce hata mafi yawan hanyoyin su na mota zuwa kauyukansu rairayin hamadar ya mamaye, wanda hakan ya sanya ba kowace mota za ta shiga kauyukan ba.
‘’Mamayar yashin hamadar ya yi tsanani fiye da kowane lokaci a sanin da muka yi, saboda a shekarun baya rairayi ya mamaye kashi 10 ne cikin dari na gonakinmu, amma yanzu ya bar mana 40 ne kawai muke iya shuka amfanin gona, sauran kashi 60 din duk yashi ne ya nutsar dasu.”
Ya ce, “A cikin wannan kashi 40 cikin dari, kashi 25 ne kawai na noman amfanin gona, kashi 15 kuma na kiwon dabbobi ne, amma ko wannan fili da muka bar shi don kiwo, wasu Fulani daga jamhuriyar Nijar sun mamaye shi don kiwon dabbobinsu kuma sun hanamu sakat a matsayinmu na yan kasa. Shima wannan wani babban kalubale ne garemu.”
“Wannan kakkarfar guguwar mai dauke da dusar kura ta na ci gaba da mamaye wa da lalata gidajenmu masu yawan gaske a yankunanmu. Haka kuma, yanzu haka da nake magana da ku katangar gidana ta rushe a karo na uku, sakamakon wannan bala’i na zaizayar hamada.”
Wakilinmu ya lura da cewa sakamakon dumamar yanayi da sauyin yanayi, guguwar yashi da kura sun ribanya, al’amarin da ya jawo karancin ruwan sama a wannan yankin, inda ya janyo farin da ake samun hatsaniya tsananin makiyaya da manoma a duk shekara.
Malam Ahmed Abubakar masani kan sauyin yanayi, ya ce jihar Yobe na daya daga cikin jahohin da ke kan gaba, wadanda ke makwabtaka da jamhuriyar Nijar, masu fuskantar kalubalen gurgusowar hamada sakamakon iskar kasurwar arewa maso gabas mai karfin gaske.
Ya kara da cewa, ‘’Yobe ta na cikin Jihohi 19 da ke kan gaba kan matsalolin gurgusowar hamada masu iyaka da Jamhuriyar Nijar, yanki ne wanda yake kan gaba a hamadar Sahara.”
“Sannnan kuma a koda yaushe al’amarin ya na yin tasiri ne sakamakon wannan sauyin yanayi wanda ya hada da iska mai dauke da kura mai gusar da rairayi, sakamakon guguwar da ke tasowa daga kasurwar Arewa Maso Gabas.”
‘’Don haka duk lokacin da wannan iskar ke tasowa ta wuce a kusan watan Nuwamba zuwa Maris a kowace shekara, muna fuskantar matsalar kura mai karfin gaske, ta na haifar da gurgusowar hamada a gurare da dama tare da kawo matsaloli daban-daban ga yankuna tare da al’ummar wadannan yankuna.”
Ya ce, mafita daya wadda ta dace wajen magance wannan matsala, ita ce dashen itace masu yawa a kowane lungu da sako. Ya ce, dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani shirin dashen itatuwa na ‘Great Green Wall’ wanda shirin ya na da nufin gina katafariyar gandun bishiyoyi a kowane bangare na kasar nan. Wanda shi ne zai bai wa muhallinmu kariya daga mummunar illar gurgusowar hamada.