Wani matashi mai shekara 29 a duniya, Ahmed Mohammed, ya shiga hannun rundunar ‘yansandan jihar Bauchi bisa zarginsa da sace wata motar kamfanin abokinsa kirar Toyota Highlander mai lamba ABC-65PK.
LEADERSHIP Hausa ta tattaro cewa, wanda ake zargin direban kamfanin wani abokin karatunsa tun a sakandari ne da ake kira Damuli Investment Company Ltd da ke garin Maiduguri a jihar Borno.
- Wani Sojan Amurka Ya Bankawa Kansa Wuta Don Nuna Goyon Bayansa Ga Falasdinawa
- Tsadar Rayuwa: NLC Ta Shiga Zanga-zanga A Adamawa
Sannan, an kuma gano cewa, Ahmed Mohammed ya arce da motar ne zuwa Bauchi da nufin sayarwa a kan kudi naira miliyan biyu, kuma abun da zai yi da kudin shi ne biyan kudin hayar gidan da zai ajiye matarsa da suka samu sabani a baya don dawo da ita dakin aurensa.
A wata sanarwa da kakakin ‘yansandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Talata, ya ce, wanda ake zargin an cafke shi ne a unguwar Bayan Gari da ke Bauchi tare da motar da ya sace.
Ya ce, “A ranar 24 ga watan Fabrairun 2024, jami’an sashin binciken sirri (SID) na rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta yi amfani da wani rahoton sirri da ta samu wajen cafke Ahmed Mohammed mai shekara 29 dan asalin yankin Polo High-Court a jihar Borno.”
Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Auwal Musa Mohammed, ya bada umarnin a zurfafa bincike har zuwa jihar Borno domin gano wasu abubuwan da suke tattare da wannan satar motar da wanda ake zargin ya yi.