Wani yaro dan shekara 16 mai suna Ibrahim Lawan ya rataye kansa a kauyen Kuki da ke karamar hukumar Bebeji a jihar Kano.
Har yanzu ba a gano dalilan da yasa yaron ya kashe kansa ba.
Jami’in hulda da jama’a na Masarautar Rano, Nasiru Habu Faragai, Hakimin Bebeji ne ya fitar da sanarwar wacce ya mika rahoton afkuwar lamarin ga mai martaba Sarkin Rano, Ambasada Kabiru Muhammad Inuwa, a yayin taron majalisar masarautar a ranar Litinin din da ta gabata.
Ya bayyana cewa, Sarkin ya ba da umarnin a kai rahoton ga ‘yan sanda da ke Masarautar domin gudanar da bincike mai zurfi kan musabbabin mutuwar.
Sai dai da aka tuntubi jami’in dan jin karin bayani kan lamarin, Faragai ya shaida wa Wakilin Daily trust cewa, Mai Unguwan kauyen yana bincikar mahaifin marigayin da nufin gano ko yaron yana shan kwayoyi ko kuma yana fama da tabin hankali.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp