Manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa biyu ne su ka gwadawa junansu kwanji a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester, wasan shi ne wasan mako na 16 a gasar Firimiya ta kasar Ingila.
An fara wasan da misalin karfe 5:30 agogon Nijeriya,da fara wasan dukan ƙungiyoyin biyu da ke hamayya da juna su ka fara kaiwa junansu hari amma babu wanda ya samu damar zura ƙwallo a raga sai a minti na 34 inda Josko Gvardiol na Manchester City ya jefawa Onana kwallo a raga.
- Pep Guardiola Ya Tsawaita Kwantiragi A Manchester City Har Zuwa Shekarar 2027
- Yau Ake Kece Raini Tsakanin Kungiyoyin Hamayya Na Manchester A Firimiyar Ingila
Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci Manchester United ta kara matsawa masu masaukin bakin kaimi har ta kai ga sun samu bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 88 wanda kyaftin din Manchester United Bruno Fernanades yayi amfani da wannan damar ya mayar da wasan danye sharkaf.
Minti biyu da ƙwallon da Bruno ya ci matsahin dan wasan Man Utd Amad Daillo ya kuma zarewa daga cikin masu tsaron bayan Man City ya jefa kwallo ta biyu da ta baiwa ba’kin damar samun dukkan maki ukun da ake bukata,kuma wannan nasara da su ka samu ya sa su darewa zuwa matsayi na 12 da maki 22 akan teburin gasar Firimiya.
Wannan rashin nasara da Manchester City ta yi shi ne rashin nasara na bakwai a wasanni goma na baya bayan nan da ta buga,kuma na uku da ta yi a filin wasanta na Etihad Stadium.