Shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma, cikin sun hadar da; Zamantakewar Aure, Rayuwar yau da kullum, Rayuwar Matasa, Soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi dubi ne game da yadda wasu iyayen suke kasa tsawatarwa yaransu idan sun aikata ba daidai ba musamman a wasu guraren.
Da yawan wasu iyayen ba sa iya tsawatarwa yaransu idan suna rashin kunya ko rashin ji, musamman idan sun tafi da su wasu guraren, sai dai su zuba ido suna ta kallonsu suna aikata ba daidai ba, kuma ba za su hana ba.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; Me za a kira hakan da shi?, Me yake janyo hakan? Ko hakan na iya janyo matsala ga yaron a nan gaba?, wanne irin matsaloli hakan zai iya haifarwa?.
Ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka: Sunana Hafsat Sa”eed Jihar Kebbi:
Ni a tunanina bata yaro ne, abin da yake janyo hakan su a nasu tunanin so kenan, basa son abin da zai bata wa yaran rai. Kwarai kuwa matsala babba ma kuwa, matsalar in yaro ya girma zai jawo mishi matsala sosai, musamman mu’amularshi da mutane. Ni shawarata shi ne; a tsawatar wa yaro ko yarinya in suna kiriniya, domin Allah ya bamu sune don mu kula da tarbiyarsu,nwannan ba gata bane ba kuma so bane, so shi ne in yaro ya yi ba daidai ba ka kwabe shi, Allah ya sa mu dace.
Sunana Ibrahim Isma’il, Jihar Kano:
Rashin tarbiyya ne kuma dole duk kaunar da kake wa da watarana sai abin ya dameka, hausawa sun ce; “ka so naka duniya ta kishi – ka ki shi dunyi ta so shi”, ma’ana idan ka bashi tarbiyya mutane za su yi alfahari da shi, amma idan baka bashi tarbiyya ba, ba iya mutane za su ki shi ba har kanka ma watarana sai ka yi da-na-sani. Shawarar da zan bawa iyaye masu irin wannan dabi’a shi ne; yin hakan ba soyayya bace, idan suna gani kamar ‘ya’yan suke so to, cutar musu da rayuwa suke kuma ko mu-jima ko mu-dade akwai gabar da za su gane haka, amma muna fatan Allah ya sa su gane su gyara ba sai lokaci ya kure ba.
Sunana Zainab Zeey Ilyas, Jihar Kaduna:
Gaskiyar magana akwai iyaye da dama wadanda suke barin yaronsu idan sun je wanu waje da su, su yi biris kamar ba yaransu ba, matar gida tayi shuru sai dai tayi hakuri idan tayi magana kuma uwar yaron ta ji ba dadi, a gaskiya ya kamata iyaye su daina nunawa yaronsu so dan wannan so ne yake janyo shi, wanda a karshe ya zamo kiyayya ga shi yaron. Dan wallahi bakin jini zai yi ni kaina bana so na ga baki sun zo gidanmu yaro yana ta kiriniya uwar yaro tayi shuru tana kallonsa, wani abun ma ko dan gida baya zuwa wajen amma haka yaron matar zai je ya janyo shi ko ya yaga irin wannan babu dadi. Ya kamata mata su sani hakan ba so bane idan ke a wajenki kin hanashi shi ne so, to ki sani a idon duniya zai zama kiyayya, Allah ya sa mu dace.
Sunana Aminu Adamu, Malam Madori A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya hakan sakaci ne da wasu iyayen suke, kuma duk yaron daya taso da irin wannan dabi’a to, tana bin sa har girman sa ya zama mara kunya, kuma su ma iyayen da suka yi sakaci abun sai ya shafe su ba zai kyale su ba, don haka ya kamata iyaye suke kula da tarbiyyar ‘ya’yansu. To wasu lokutan makauniyar soyayyar da iyaye suke nunawa ‘ya ‘ya su ne ke jawo haka, ta sa basa son bacin ran ‘ya ‘ya su komai suka yi daidai ne a wajen su, a wasu lokuta kuma sakacin kula da tarbiyya ne da iyaye maza suke, shi ke jawo wannan matsala. Domin iyaye Mata kadai basa gudanar da tarbiyyar yara sai da gudunmawar iyaye maza tarbiyya ingantacciya take samu. Sosai ma hakan yana zama matsala ga rayuwar yara, domin rayuwa bata hawa kan saiti sai da tarbiyya, domin sai da tarbiyya mutum zai san daidai da kuma ba daidai ba, kuma sai da tarbiyya yaro zai san mutuncin kansa kuma yas an na iyayensa da ma sauran al’umma. To da farko dai al’umma za su na kuka da yaro har suke guje masa domin tsira da mutuncin su, na biyu kuma ku iyayensa ba za ku tsira ba daga sakamakon rashin tarbiyyar sa, daga karshe kuma zai iya fadawa munanan dabi’u kama daga shaye-shaye, sata dai dai sauransu. To farko ya kamata su sani ‘ya ‘ya amana ce Allah ya basu kuma zai tambaye su akan ta, kuma duk lokacin da iyaye suka bawa ‘ya’yansu tarbiyya ta gari to kamar sun saka hannun jari ne, Allah kadai ya san irin yawan ribar da za su rinka samu.
Sunana Na’ima Sulaiman, Jihar Bauchi:
Eh! Hakan yana faruwa dan mun taba zuwa gidan amarya kawai yaron wata mata ya yaga ledar kujerun, kuma uwar yaron na kallo sai tayi ‘yar dariya tana cewa “Wane kenan”, To, yanzu irin hakan idan har daman ba farke su ake shirin yi ba ai ya jaja mata, a hakan ma duk da amfani za a yi da su kuma ba a zo jere ba an dai zube an ajjiye ne kawai kuma ya yaga, madadin ta hana shi tun kafin ya aikata amma sai tayi shuru ta zuba masa ido har ya je ya aikata, karshe ma ta bi shi da dariya kamar wanda ya aikata wani abun arziki, wanda kowa bin su ya yi da kallo. Babban abin da ke janyo hakan rashin tarbiyya ce wanda iyaye mata suke kasa bawa yaransu ita. Dan haka yana da kyau mata a rinka kulawa da tarbiyyar yara dan gudun da-na-sani watan watarana.
Sunana Muhammad Isah, Zareku Miga LGA Jihar Jigawa:
Na farko dai duk yaron/yarinyar da yake irin wannan akwai baci da kuma saka ci a wajen iyayen. Sannan yana janyo yaron ko yarinyar su zama hakan dalilin rashin kwabar yaro ko yarinya tun da farko kafin ya kai wani mizani. Kwarai kuwa zai iya janyo matsala yaron zai zamo fitinan ne marar jin maganar kowa. Matsalolin da hakan zai janyo shi ne yaron zai zamo marar ji a unguwa kuma zai fitini ‘yan unguwa, musamman gidan daya je bakunta. Dafarko dai shawarar da zan bawa iyaye anan ya kamata suna hana ‘ya’yansu abun da bai kamata ba tun suna yara, sannan kuma su hanasu mu’amula da irin wannan yaron marasa ji da kiriniya.