Wasu kwararrun likitoci a asibitin kula da lafiyar mata da kananan yara mallakar da ke Damaturu a Jihar Yobe, sun samu nasarar yi wa wasu mata masu juna biyu tiyata, inda kowace ta haifi jarirai shida-shida.
An ruwaito cewa, matan wadanda suka fito daga yankuna daban-daban, sun haihu ne a makon da ya wuce, inda suka shafe sati biyar ana duba lafiyarsu a dakin kulawa na musamman.
- Dan Kwallo Ya Mutu Ana Tsaka Da Wasa A Filin Kwallo A LegasÂ
- EFCC Ta Kwato Motoci 15 Da Na’u’rori Daga Hannun Masu Damfarar Yanar Giolzo A Wari
Likitocin sai da suka bi dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da sun yi wa matan tiyata cikin nasara.
Jariran sun kasance kowanne su na da nauyin kilo 2.0, inda daya kuma yake da nauyin da ya kai kilo 2.7.
Masu jegon sun gode wa likitocin da sauran ma’aikatan jinya na asibitin kan kokarin da suka yi, inda kuma suka yaba wa gwamnan Jihar Mai Mala Buni kan samar da ingantattun kayan aiki a asibitin.