Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zaƙulo muku batutuwa daban-daban, waɗanda suka shafi al’umma. Ciki sun haɗar da; zamantakewar aure, rayuwar yau da kullum, rayuwar matasa, soyayya, da dai sauransu.
Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu matan suke yi wa mazajensu gwaji a waya, gudun kada su yi musu kishiya. Misali; Mace za ta ari wayar wata ta riƙa chat da mijinta da zummar wata ce daban, ta fara soyayya da shi dan ta gwada yana kula wata ko ba ya yi.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin ma’abota shafin game da wannan batu “Wane irin kira za a yi game da irin waɗannan matan?, Ko akwai wasu illoli/matsaloli da hakan zai iya haifarwa?, Wacce shawara za a bawa masu aikata hakan?”
- Na Dauki Fim Sana’a, Duk Alakata Da Kai Sai Ka Biya Kafin Na Yi – Asiya Auta
- Sirrin Albasa Wajen Inganta Lafiyar Dan Adam
Ga dai bayanan nasu kamar haka:
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga Jihar Kano:
Wannan yana faruwa sosai gaskiya, kuma ƙarshe ba a wayewa da lafiya gaskiya. Masu yi gaskiya tun wuri su daina wallahi, dan aure ya sha mutuwa ta sanadin haka ƙarshe azo ana nadama mara amfani. Sosai ana samun gagarumar matsala tsakanin ma’aurata zargi ya shiga tsakani, daga nan ma dai wani aure ka ji ya mutu. Su yi wa kansu faɗa, su daina gaskiya.
Sunana Haj. Maryama Ahmad, daga Jihar Kaduna:
Wannan matsaloli suna faruwa sosai, kuma rashin tunani ne yake janyo hakan. Dalili kuwa ko da namiji ba shi da wannan tunanin na soyayya da wata to, kin ƙirƙirar masa ke da kanka, kin riga da kin nemo masa hanyar da zai riƙa samun damar bibiyar wasu. Haka lambar da za ki ara ko da ace ita macen ba ta bibiye shi ba, watarana zai ji yana son bibiyar lambar musamman lokacin da ki ka ɓata masa, sharrin ɗa namiji na da yawa ya san hanyoyin da dama waɗanda zai bi ya tursasa ita wannan me lambar ko da kuwa ba ta buƙatar sauraronshi har sai ya cimma burinshi. Kin ga kenan kin kawo wa kanki da kanki wata masifar kuna zaune lafiya ke da mijinki, Allah dai ya kyauta. Wannan darasi ne babba musamman ga ƴ an’uwa mata manya da yara, dan wata babbar kamar ƙaramar yarinya haka take. Allah ya sa mu dace.
Sunana Fadila Lamiɗo daga Jihar Kaduna:
In ban da ganganci akan wani dalili za ki ɗauki ‘number’ mijinki ki saka a wayar wata? wannan tamkar bawa mage ajiyar kifi ne, idan ma kina tunanin kin goge ‘number’ bayan kin gama ne shi mijin naki yau da gobe kina masa haka zai iya bin bayan ‘number’ don shi ba walliyi bane, garin neman gira sai a rasa ido. Ina kira ga mata su guji tsananta buncike, su sa a zuciyarsu kishiya ƙaddara ce kuma bawa baya iya gujewa ƙaddararsa. Su mayar da hankali wajen roƙon Allah abin da suke so wa kan su na alheri, in sha Allahu Allah zai shiga cikin lamarinsu, ba tare da sun ɗaga wa kansu hankali ba, wajen binciko abin da ka iya kawo masu rashin kwanciyar hankali.
Sunana Princess Fatimah Mazadu, daga Jihar Gomben Nigeria:
Tirƙashi kin san wauta da dolanci wallahi wannan shi ne, kat! ah to, in ba wauta ba ke kin isa ki gama sanin ɗa namiji? Ko chat da neman hanyoyi ta zamani za ta isar miki ki gane halayen mijinki ko sanin ƴ an matanshi ko neman aurenshi da makamantansu?. Ai tonon asiri ne da rashin sanin zafin kai, da ƙoƙarin saka zargi tsakanin zamantakewarku. Ai kira da babbar murya in har akwai masu niyyya ma wallahi kar su kuskura, dan wata in ta yi ta wanye lafiya, wata gidansu za a korata. Shurme ne sosai ace wai mace tana bibiyar namiji akan dole ta san ainihin abun da ke tafiya a rayuwarshi, an ce mana mazan daƙiƙai ne? ai sun fi mu wayewa a wannan fannin. Tunda dai ban taɓa jin an ce ga mace ta ƙirƙiri Tiktok ko Facebook ko Instagram ba, kawai ki kasance mai yadda da shi akowani hali idan bai saɓawa addininmu. Matsaloli kam, ai ba adadi dan garin gwadashi wallahi za ki gwado bala’i a ƙoƙarinki na ki san meke tafiya, kawai ana cikin hira ya ce misali “yau ina komawa ma zan saki matata tun da zan mallakeki…” Dan Allah ya za ki yi? Shin za ki tonawa kanki asiri ne, ko za ki cigaba da chat ɗin?, ko daga ya dawo za ki tare shi?, ko za ki hau haɗa kayanki ne?, kin ga wannan ƙaramin misali ne, wallahi mata su kiyayye wannan shurme ne. Matsaloli kamar; rashin kwanciyar hankali, zargin juna, nadama, da-na-sani, banzar aƙida.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Rano LGA Jihar Kano:
Idan za a yi ba mai zurfi ba, kuma za a yi gwajin da zuciya ɗaya bada niyyar tayar da fitina ba a nawa fahimtar babu matsala. Akwaisu matsaloli kam, idan har ita cen ta fiye gwajin mai zurfi. Shawarata a nan ita ce, kawai duk wata mace tana yi wa mijinta kyakykyawan zato musamman akan ƙarin aure, domin Allah ne da kansa ya halastawa namiji ya auri mace har guda huɗu amma fa idan zai yi adalci, shi kuma adalci ubangijinmu ne kaɗai mai yinsa daidai. Allah kasa mu dace amin.
Sunana Hadiza Ibrahim D. Auta, Ɗaura-Namoda Jihar Zamfara:
Babban ƙalubale ne ga mata masu irin wannan halin bin diddigi, ko ga namiji ballantana ga mace wadda ba ta isa ta saka ko ta hana ba. Kira na ga masu irin wannan halin su daina gwajin su tsayar da hankalinsu a kan abin da suka gani zahiri. Saboda Allah da kansa ma ya ce kada mu tsananta bincike, gudun garin tone-tone kaza ta tono wuƙar yanka ta. Akwai illoli masu tarin yawa dangane da matsalolin da wannan gwajin yake haifarwa ga masu riƙo da shi a matsayin wayewa, ko babban makamin da suke riƙo da shi domin tabbatar ko gano; ana son su ko ba a son su, kuma mijinsu yana kula wasu matan ko babu ruwansa da su. Saboda ba a gwada namiji da mace komai muninta. Don akwai wata da ta taɓa saka ƙawarta ta yi wa saurayinta gwajin; daga haka aure ya ƙullu a tsakaninsu ya bar budurwarsa ta asali ya auri ƙawarta. Haka ma ƙawa ta taɓa kwace mijin ƙawarta a irin wannan gwajin daga wasa. Shawarata ga masu yi kawai su daina, a wannan zamanin da muke ciki miji ko saurayi duka ɓoye su ake yi kamar an samu kuɗi. Wata ko ba a saka ta yin gwajin ba gaban kanta take yi, idan ta samu dama sai dai ƙawar ta ji labari a sama zancen ya sauya, mai son ta ya koma kan ƙawarta ko kuma ƙawarta za ta aure mata miji.
Sunana Muktari Sabo, Jahun A Jihar Jigawa:
Mata mutanenmu lallai hakan tana faruwa wato mace take bibiyar mijinta ta hanyoyi mabambanta ciki kuma har ta waya. Kiran da zan yi akan haka shi ne, mata su ji tsoron Allah kuma su sani bibiyar ba abin da za ta hana wanda Allah ya sa zai faru. Akwai matsaloli; na farko dai ta ɗorawa kanta rashin kwanciyar hankali, sannan hakan zai iya haifar mata matsala tsakaninta da mijinta. Shawara a nan ita ce mata masu wannan hali su daina, domin yin hakan ba zai hana ayi musu abin da suke tsoro ba wato kishiya.
Sunana Hafsat Sa’eed, daga Jihar Neja:
A nawa tunanin hakan bai kamata ba, mace ta gwada kiran mijinta matsayin wata daban, duk abin da ya je ya zo kuwa ita ta jaho. Dan wannan kowaye ya ji ya san dole a samu matsala a gaba, kuma abin da macen ke tsoro za ta iya janyo shi da kanta. Idan ma zargi take kan yana aikata wani abun, sai ta barshi shi da ubangijinsa ya fi mata.
Sunana Hauwa Abubakar Sarki, daga Suleja Jihar Neja:
Kishi na iya sa mace ta aikata komai, duk yadda mace ta kai ga bin diddigin mijinta da sanya ido akan al’muransa, wai dan saboda kada ya ƙara aure yayyo mata kishiya wallahi aikin banza ne. Idan mijinki ya yi niyyar aikata abu musamman ƙara aure kuma bai yi niyyar gaya maki ba duk buncikenki ba za ki taɓa ganewa ba. Kiran da zan yi a gare su shi ne su bari, duk abin ki, baki isa ki hana namiji abun da yayi niyya ba. Musamman akan ƙarin aure, addu’a da miƙa al’amura zuwa ga Allah shi ne kaɗai mafita a gare mu. Sosai kuwa, illah ta farko shi ne, idan har ki ka kamasa da abin da ki ke zargin yana aikatawa babu abun da zai haifar maki sai tashin hankali. Shawarar da zan basu shi ne, idan har ba saɓon Allah yake da wanda yake neman ba mafi a’ala shi ne ki bi shi da fatan alkhairi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp