Barkan ku da kasancewa tare da shafin TASKIRA, shafin da ke zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da yadda wasu ‘yan matan ke zuwa wajen saurayi da kuma gidan surukai.
A lokutan baya kadan da suka shude, samari ne ke zuwa wajen ‘yan mata da sunan zance, duk da cewa akan samu daidaikun wasu yaran da suke iya zuwa wajen saurayi gidansu ko kuma shagonsa da sunan zancen, sabanin shi ya je.
Sai dai kuma a yanzu labarin ya sha bamban da na baya, domin kuwa zamani ya kara hure wa mafi yawan ‘yan mata kunne wajen yawan kai ziyara ko zuwa zance wajen saurayi, wanda hakan suke kallonsa da sunan wayewa, hadi da yawan zuwa gidan surukan da babu tabbacin zamansu surukai ga yarinyar, wanda a karshe iyayen yaron har ta kai ga sun gargade ta da kada ta kara zuwa gidan nemansa ko kuma gaishe su, gudun kar ta bata musu tarbiyyar yaro.
Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin; Shin hakan abu ne mai kyau ko mara kyau? Wanne riba ko rashin riba hakan ke da shi, wanne irin matsaloli hakan ke iya haifarwa? Ta wacce hanya ya kamata a magance afkuwar hakan?.
Mabiya shafin sun bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Sunana Aminu Adamu Malam Madori, Jihar Jigawa:
Eh! to zuwa wajen saurayi akai-akai a wajen budurwa sam-sam bai dace ba, domin hakan zabar da kima ne, amma idan da dalili kamar dubiya ta rashin lafiya, gaisuwar mutuwa ko jaje duk babu laifi. Zuwa gaida mahaifiyar saurayi ma ba laifi ba ne, domin kyautatawa ce. Tabbas! hakan ba abu ne mai kyau ba, muddin za take zuwa akai-akai to shi kanshi saurayin zai daina ganinta da kima ko daraja, haka zalika ‘yan uwan saurayin da ma sauran Al’umma, kuma haka ka iya bude kofar faruwar wata barna da za a iya sabawa Allah. To magana ta gaskiya hanyar magance wannan matsala daya ce; iyaye su bawa ‘ya’yansu cikakkiyar tarbiyya da nuna musu mutuncin ‘ya mace shi ne kama kai da kuma duk mai sonta ya zo gidansu ba wai ta je gurinsa ba, domin shi ne yake neman aurenta ba ita ce take neman aurensa ba.Ta bangaren samari kuma a ji tsoron Allah domin kai ma wata rana uba ne ba za kaso ‘yar ka take zuwa wajen wani ba. To da farko dai iyaye su dage wajen yi wa ‘ya’yansu tarbiyya da kuma addu’ar shiriya don Allah ya shirya musu. ‘Yan mata ku sani mutuncin ‘ya mace shi ne a bita gidansu domin neman aurenta ba wai take bin saurayi ba. Su kuma samari su ji tsoron Allah su sani su ma wata rana iyaye ne kuma duk abun da ka yi wa ‘ya”yan wasu kai ma sai an yi wa ‘ya’yanka, daga karshe nake addu’ar Allah ya sa mu dace duniya da lahira.
Sunana Fatima Jaafar Abbas, Jihar Kano, Karamar Hukumar Rimin Gado:
Gaskiya a al’adar bahaushe hakan ba abu bane mai kyau, domin hakan na nuna rashin kunya wanda kunya tana tare da Imani, don haka a mahangar sharia za mu iya cewa ba abu bane mai kyau. Hakan zai haifar da matsaloli kamar zubar da mutunci don duk mai mutumci ba za ta bi saurayi ba koda tanada shi mutane za su yi mata wani kallo, rashin kima a idon uwar saurayin. Hanyar daya kamata a magance shi ne ta hanyar fadakarwa da nunawa ‘yan mata illar hakan. Shawarar da zan bawa iyaye shi ne su dinga sa ido akan ‘ya’yansu, su kuma ‘yan mata su kula da kimar su wadda musulunci ya basu, su kuma samari ba ajinka bane ka bari mace tana binka kai ma darajarka da kimarka za ta zube don haka aji tsoron Allah baki daya.
Sunana Muttaka (M.T.K) Shawu, Takai Jihar Kano:
Hakika wannan akwai garari sosai budurwa ta ringa zuwa gurin saurayi zance, domin karkashin hakan ta bangaren budurwar na iya fuskantar barazanar tarbiyyarta ta gurbata. Na iya jawo wa ita budurwar ta bujirewa umarnin iyayenta da kuma bin duk wani sharadi da saurayin zai gindaya mata koda kuwa ya sabawa addini, al’ada da tunani mai kyau wanda hakan zai tarwatsa rayuwarta. Dole sai iyaye sun sanya ido akan ‘ya’yansu dan sanin dawa – dawa yaransu suke alaka da kuma nuna musu cewa lallai na-da muhimmancin gaske sanar da iyaye koma waye ya shigo rayuwarsu, to lallai sai iyayen nan sun sani wannan zai taimaka kwarai da gaske. Lallai iyaye su sani ‘ya’ya amana ce Allah ya basu kuma zai tambaye su akai. Samari da ‘yan mata su ringa tunawa duk abin da suka aikata mai kyau ko marar kyau Allah na kallonsu, kuma duk abin da su kai su ma zuwa gaba yaran da suka haifa za su yi musu, Allah ya sa mu gyara.
Sunana Sadiya S. Girl, Jihar Kano:
Gaskiya wannan ba abu ne me kyau ba duba da al’adunmu na Hausa Fulani yara mata da kunya aka san mu, yin hakan rashin kunya ne, ai wannan ba maganar abu me kyau wallahi babu kyau, saboda ita kunya ai nau’ine na mace ta gari to ta ya ya mace tana haikewa namiji har tana binsa gida sannan ace wannan ita ce za ta yi wa yara tarbiyya watarana?,
Ni dai a ganina hanya daya ce wajen nagance wannan matsala:- iyaye mata mu kula mu tsaida hankulanmu kan yaranmu mata mu nuna musu dabi’ar da ta dace dasu wadda za ta sa ayi alfahari dasu, sannan mu haska musu wadanda suka aikata hakan ribar me suka samu a karshe? za su ga auren ma basa ganin nutuncin juna bare girmamawa. Shawarata ita ce; Mu mata mu kasance masu aji, mu nunawa maza mu fa a gidajen iyayenmu kamar ‘yan sarauta muke, munada izza, munada isa ko zuwa ya yi sai mun yi yauki munja aji kafin mu fito, muna gwalli, idan har suka ga hakan sun san ma ke me mutunci ce ba za ki biyewa wannan shashancin ba bare har ki tafi zuwa gare shi.
Sunana Lawan Isma’il (ABU AMFUSAMU) Jihar Kano, Karamar Hukumar Rano:
Maganar gaskiya addini ban san inda ya hana hakan ba amma a Al’adarmu ta hausawa kuma ‘yan arewa hakan abu ne mara kyau a namu al’adar. Ire-iren matsalolin da hakan yake haifarwa shi ne mafiya mazan ba sa rike matan da muhimmanci idan ma fa Allah ya sa an yi auren, sannan kuma yana yawan kawo gurbata tarbiyyar maza da matan. Akwai hanyoyi amma mafi sauki ita ce ke mace ki yi kokarin kare mutuncinki dana iyayenki, da addininki, da kuma al’adarki, ki tsaya a inda kike saurayinki yana zuwa inda ki ke indai fira ce ba wani uzuri na daban ba. Shawarata anan ita ce iyaye su tsaya su saka ido sosai akan yaransu ba wai iya iyayen ‘yan matan ba har da iyayen samarin, domin su kansu iyayen yaron ba za su so ace sunada budurwa tana zuwa wajen saurayi fira ba, kuma kai ma saurayin haka ka kaddara wannan diyarka ce haka ke ma ba za ki so ace kina da diya mace tayi irin wannan haukan ba, ya kamata muna jin tsoron Allah a dukkan al’amuranmu Allah kasa mu dace.
Sunana Maimuna Shuraihu, Jihar Kaduna:
Gaskiya babu kyau, matsalolin da yake kawowa na daya yana sa rashin tarbiyya, sannan ya kansa saurayi ya fara neman yarinya ta hanyar da bai dace ba, kuma yana sa mutuncin yarinya ya zube, a zamanin ‘da’ yarinya idon ana sonta ko ta hanyan gidan mutane bata bi balle ta shiga gidan ko ta je wajenshi. Hanyar da ya kamata a magance matsalar shi ne; yin wa yara nasiha da nuna musu ba abu bane mai kyau, sanan kuma mu yawaita addu’a. Ni dai shawarar da zan bada shi ne iyaye su ringa sa ido akan yayansu mata, kuma su san ina ne inda suke zuwa, kuma da wane ne suke tare, sannan ku maza ku ji tsoron Allah ku daina bari ana zuwa wajenku sabida wallahi duk abun da kai wa ‘yar wani wallahi sai an yi wa naka ko mu-ji-ma ko mu-dade, Allah ya kare ya shirya mana zuria da mu baki daya.
Sunana Sunana Ibrahim Ismail:
Gaskiya ba daidai bane kuskure ne mai girma, kuma gaskiya duk rashin tarbiyya ne, kuma abin yana da illah sosai duba da namiji wani za ki ga akwai masu yaudara wanda zai amfani wurin kai hari kamar aura zai yi, bukatarshi tana biya zai bar abin da ya bayar ya gama da yarinya ballantana kuma ba abin da akai muku da namiji ki dinga zuwa wurinshi. Hakan yana haifar da badala kuma mu maza mu tuna komai kayi sai an yi wa naka. Yadda za a magance matsalar shi ne iyaya su tashi ka-in da na-in wurin kula da yayansu, Allah ya shiryar baki daya.
Sunana Zainab Zeey Iliyasu, Jihar Kaduna:
Hakan kwata-kwata ba abu mai kyau bane, saboda hakan yana nuna rashin kunya da rashin tarbiyya, domin kunya na daga cikin imani, wadansu iyayen basu yarda da ma ‘yarsu ta fita zance ba balle ma har ta sa kafa ta je wai gidan surukai da saurayi ba tare da shirin aure ba, yin hakan yana haifar da da mara ido. Hakan bai dace ba yana jawo matsololi da dama musamman bayan aure, sannan yana sa namijin ya ji macen ta gundure shi tun kafin ayi aure, kuma koda ace an yi auren iyayen mijin nata za su gane ita mai kunya ce ko akasin haka. Iyaye su dinga sa ido a shige da ficen ‘ya’yansu mata sosai, su hane su da zuwa gidan surukai, su nusar da su matsalolin da ke faruwa in anje wajen saurayu da gidan surukai. ‘Yan mata su daina zuwa wajen saurati dan kar ya kai ki ya baro ki, domin hakan zai iya jawo gagarumar matsala wan da za su zo suna dana sani, ta masu iya magana suka ce da-na-sani keya ca, wanda ba za su iya dawo da baya su gyara ta ba, iyaye kuwa su hana yaransu yawan yawace-yawace shi yake janyo wa har yarinya ta tafi ba a dan ma ta je can din ba.