Yayin da yajin aikin gargadi na kasa baki daya da kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta kira ya shiga rana ta biyu, iyalai sun fara kwashe ‘yan uwansu daga asibitocin gwamnati zuwa masu zaman kansu a jihar Filato.
A Asibitin Kwararru na Jihar Filato, dogon layin masu amsar katin asibiti don neman kulawa da lafiyarsu ya yi batan dabo a lokacin da wakilinmu ya ziyarci asibitin.
- Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu
- Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka
Wata mata mai suna Misis Mary David, wacce ta yi rajista a asibitin duba lafiyar mata masu juna biyu, ta shaida wa wakilinmu cewa babu ma’aikatan jinya da za su duba ta da sauran wadanda aka shirya za a duba su a ranar Alhamis.
Da aka tambaye ta game da matakin da za ta dauka na gaba, Misis David ta ce za ta koma gida har sai an dakatar da yajin aikin.
Mista Nde Danladi John daga karamar hukumar Kanke wanda shi ma ya zo ya kwashe iyalinsa, ya ce babu wanda ya duba su a asibiti tun ranar Laraba.
Haka kuma, a sashen kula da lafiya na matakin farko na Jos ta Arewa da Jos ta Kudu, ba a ga wata ma’aikaciyar jinya da ke kula da marasa lafiya ba yayin da likitan da ke bakin aiki ya halarci wasu tsirarun marasa lafiya, ya ce sauran su dawo ranar Juma’a.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, yajin aikin da aka fara da tsakar daren ranar 30 ga watan Yuli, 2025, ya janyo janyewar ma’aikatan jinya da ungozoma baki daya a dukkanin cibiyoyin lafiya na tarayya da ke fadin kasar nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp