Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a yankin Kugauta da ke Kusheka, da kuma Kitanda da ke Geshere a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna tare da yin garkuwa da mutane 22.
Wani Dalibin Majami’a kuma mazaunin garin Emmanuel Johnson, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da manema labarai ta wayar tarho a Kaduna, ya ce ‘yan bindigar sun mamaye al’ummomin biyu ne a wasu hare-hare a daren Juma’a da misalin karfe 10:30 na dare, inda suka yi garkuwa da mutanen wanda mafi yawancinsu mata da kananan yara ne.
- Rikicin Ƙabilanci Da Saɓanin Makiyaya Da Manoma Ya Zama Tarihi A Jihar Kaduna – KSPC
- Mutane Da Dama Sun Rasu Sakamakon Bindigar Tankar Mai A Enugu
Ya tabbatar da cewa, an yi garkuwa da mutanen 12 a yankin Kitanda da ke Geshere, yayin da wasu 10 kuma aka yi garkuwa da su daga yankin Kugauta na Kusheka.
Ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna (PPRO), DSP Mansir Hassan ba da aka tuntube shi har zuwa lokacin hada wannan rahoto.