Assalamualaikum jama’a barkan mu da warhaka, sana’a sa’a in ji Hausawa kuma an ce ‘Mai talla shi ke da riba.’ To a yau za mu ga yadda ake bude kamfanin sayar da abinci ko abin sha.
Idan mutum zai yi sana’a ya kamata ya lura da irin sana’ar da ke da samu kuma wanda ake yawan amfani da ita. Abin da ake yawan amfani da shi ko kuma in ce ba mu iya rayuwa in ba tare da shi ba shi ne abinci.
- Majalisa Ta Tabbatar Da Arase A Matsayin Sabon Shugaban Hukumar Kula Da ‘Yansanda
- Qin Gang Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Ma’aikatar Harkokin Wajen Gabon Bisa Rasuwar Ministan Harkokin Wajen Kasar Michael Moussa-Adamo
Bude kamfani kasuwanci ne wanda mutum zai shiga yana da kyau ya tsaya ya yi tunani me zai yi wanda zai ja hankalin mutane wanda ake ci ko kuma sha.
Kamfanin abinci sun fi samun kudi saboda kullum dole mutum ya ci ko kuma ya sha shi ya sa kafin ka shiga kasuwa ka tsaya ka duba shin sabon abu za ka kawo ko kuma gyara ne ka ke son kawowa inda ka ga akwai matsala.
Gyarawa wato zama unikue game da sauki shi ke jawo mutane su so abin da kake kuma suna ba wasu shawarar saya ko tallata maka haajarka.
Kafin ka bude kowace masanaantar kasuwanci a Nijeriya wanda ya shafi ci ko sha ko kuma kowace sana’a ya kamata ka na da business plan (wato tsarin kasuwanci). tsarin kasuwanci ya na taimakawa sosai saboda ta hanyar shi ne kawai za ka iya fahimtar inda kasuwancinka ya dosa, saboda zai kunshi su waye kwastomominka masu saye kuma su waye ke rige-rige wato ‘Competitors’ dinka a irin kasuwancin, kuma ya za ka fi su.
Bayan haka kuma ta hanyar ne za ka fahimci wane tsari za ka yi ma kasuwancin yadda zai tafi a farko da kuma abin da ake son cimmawa a nan gaba duk ta shi ne ake ganewa.
Register NAFDAC:
Abu na gaba shi ne rajista da samun dama daga NAFDAC wadda Hkuma ce da ke kula da kasuwanci ko kamfanonin da ake kokarin kafawa a Nijeriya da suke sarrafa abinci ko kuma abin sha ko kuma suke hada magani.
Mallakar CAC
Mallakar wannan lambar na da matukar muhimmanci saboda ita ce mutum zai iya samun cikakkiyar shedar kasuwancinsa a Nijeriya.
Wannan lambar na da kyau sosai saboda idan ka yi la’akari ko tallafi, rance ko wane samun jari da gwamnati take badawa dole sai da ita wanda ba shi da ita kusan baya cikin lissafi.
Abu na gaba shi ne kulawa
Kowane nau’in kasuwanci ya na son kulawa musamman ma abinci da abin sha saboda mutane da yawa za su sa ne a cikinsu.
Kulawa ta shafi tsaftar kayan masarufi, yanayin tsaftar ma’aikata da kiyaye hakkinsu, sai kuma a tsaftace muhalli saboda gudun cututtuka da ke iya shafar abin wanda ana iya yada mutane da yawa da ba’a ma san iya adadinsu ba.
Allah ya taimaka ya bamu sa’a ya albarkaci nemanmu don girman zatinsa.