Yaya Amarya Za Ta Gyara Mamanta?
To abin da za ki fara yi shi ne, ki fahimci mamanki yaya yake wato shape dinsa da kuma rigarsa ( breziya ) da zaki rika sakawa.
- Akwai mai mango mama mai kama da mango ( shi ne wanda kansa yake kallon sama) irin wannan maman ba ya zubewa da wuri, irin wannan ba ta shan wahalar gyara.
2 Sai kuma mikakke (shi ne za ku ga yana kallon gaba wato (straight ). Gaskiya irin wannan maman yana saurin faduwa, kuma me wannan ta rika shan kunun Alkama musamman idan sun fara kwanciyar.
3 kwai mama mai kallon gefe zakuga akwai nisa sosai a tsakinin maman biyu kuma maman har ya kusa shiga hammata.
Irin wannan maman ma yakan zan kwana biyu bai zube ba, mai irin wannan mama dole, ta rinka amfani da rigarsa ( breziya ) din da kada kwaba tsakanin Biyu na (breziya). Amma sauran kala biyu na farko za su Iya amfani da rigar mama wanda kawai za ta yi musu dai-dai, amma ba’a son mace ta rinka saka rigar mama wanda ya matse mata mama saboda zai rika danne ginshikin mamanta kuma daga nan ya yi laushi mako daya .
To dole mamanta ya fadi, ku rika sayan (breziya) mai fadin hannu da baya saboda ya fi hada taimako fiye da mai siraran hannu da bashi da fadin. Yanzu ga wani hadin wanda tuntuni matan birni da na kauye suke amfani da shi wannan hadin shi ne za ki yi.
Idan kin ga mamanki ya zama kanana kina so ya ciko kamar balan-balan to ki gwada wannan. Za ki shanya Aya ta bushe sai ki hada ta da garin Alkama da farar shinkafa da Aya da gwada duk ki jika su ki markada, sai ki tace ruwan sannan ki sake dorawa a kan wuta sai ki saka sauran kayan hadin wato zuma da madara kowacce saboda ya yi kauri kina juyawa a kan wuta.
Daga ya yi dan kauri kadan sai ki juye kina sha kullum sau 2 a rana.
Za mu ci gaba mako mai zuwa