Assalamu alaikum masu karatu, barkan mu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Uwargida Sarautar Mata.
A yau shafin na mu zai zo muku da yadda uwargida za ta ja hankalin maigida a lokacin da take bukatarsa alhali shi kuma babu sha’awa a tare da shi.
Mata da yawa sukan shiga damuwa, wasu ma su bata rai, akwai wadnda hakan ya kan zamo musu matsala a lokacin da suke da bukatar mazansu, su kuwa mazan ba su da bukatarsu.
Duk kuwa da ana samun matan da mazan ke da bukatansu su kuma a wannan lokacin ba su da bukatar mazan nasu. Sai dai hakan ya fi yawaita ne ga maza ganin su ne mafi akasari suke shiga yanayin da sha’awar jima’i yakan dauke musu.
Gajiya, bacin rai, fargaba, rashi da zullumi, duk wadannan sukan iya kwantar wa mutum sha’awarsa ta Jima’i, wanda akasarin wadan nan yanayin sun fi shafar maza.
A duk lokacin da mijinki ya dawo ya nuna miki alamu ko kai tsaye bai da sha’awar Jima’i ga shi ke kuma kina hannu, ka da ranki ya baci ko ki yi fushi da shi. Ko ki soma zargi ko furta kalamai marasa dadi ga mijinki kamar yadda wasu matan suke yi. Ga wasu dabarun da za ki gwada domin janyo hankalinsa cikin sauki.
Sa shi ya yi wanka: Kasala na daya daga cikin abubuwan da ke kwantar wa namiji sha’awar Jima’i. Don haka da zaran kin fahimci mijinki ya shigo jikinsa a mace, yi kokarin tanadar masa abin da zai yi wanka da shi.
Idan kuma dama kayan wanka na zamani kuke da shi a gidanku. Jawo hankalinsa ya zuba ruwa a jikinsa domin samun karfi a jikinsa.
Shirya Masa Kayan Shayi: Yana fitowa daga wanka abu na gaba da zai sa mijinki ya warware shi ne shayi mai dumi kafin ko bayan cin abinci ko kuma lokacin da yake cin abinci.
Kada ki sake ki hada masa shayi da madara muddin ba za a saka masa nascafe bane a cikin shayin. Domin ita madara zalla a shayi tana kara kashe jiki ne ga mutumin dake son yin bacci mai dadi. Don haka Lipton tea ko hadin nascafe shi ne abin da za ki hada wa mijinki.
Lipton tea ko Nascafe suna kara kuzari a jiki, kuma su gusar da gajiya ko kasala da mutum yake ji sannan su tsaiwaita masa lokacin da bacci zai dauke shi. Kin ga a nan kin yi hanyar da dole sai ya dauki lokaci kafin bacci ya dauke shi.
Idan kuwa shi ba mai shan shayi bane, to akwai lemun kwalba ko na gwangwani dake kara kuzari irinsu power horse dama na leda irin su passion kina iya zuba masa cikin ruwan da zai sha bayan cin abinci domin ya wattsake.
Tausa: Cikin dabarunki na motsa sha’awar miji ya kwantar miki da naki sha’awar shi ne ki masa tausa. Kina soma yi masa tausan ne tun a lokacin da yake zaune yana cin abinci ko shan shayi.
Wuyansa, kansa da kuma kafadunsa su ne abin maida hankali wajen yi masa tausa a wannan lokacin. Daga nan idan doguwar kujera ce da ku kuma akwai sarari mike shi a kai. Idan kuma babu halin hakan nan jawo shi cikin daki. Ki tabbatar a kwabe yake ki soma masa tausar a ruf da ciki.
Ki kasance mai kwantar masa da hankali idan da wata damuwa ce ya shigo, idan kuma da gajiya ce nan ma kina yi masa tausar kina yi masa kalamai masu ratsa zuciya cikin tattausar murya.
A lokacin da za ki juwo shi ya dawo ringingine tuni sha’awarsa ta tashi. Cikin sauki da kwanciyar hankali ba tare da bacin rai ko fushi ba ya zo hannu sai kuma yadda kika yi da shi daga wannan matakin.
Akwai matan da kai tsaye suke nuna wa namiji suna bukatarsa ba tare da wasu dabaru na motsa shi ba, hakan zai yi wahala da fatar baka kadai ki motsa wa namijin da bai da niyya da kuma sha’awar Jima’i sha’awa.