Assalamu alaikum masu karatu, barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Ado Da Kwalliya.
Ciwon Sanyi wato (infection), wani ciwo ne da yake addabar mata a wannan zamani, gashi ki ga a yi ta magani amma ba ya jin magani in ba Allah ya sa an dace ba, sannan kuma yana sa fitar wani ruwa mai wari a gaban mace da kuraje, wani ma ki ga ya yi ja tsabar susa, Sannan kuma yana kawo wa mata cikas lokaci jima’i wasu suna jin zafi sosai har yasanya wata ma za ki ga tana gudun mijinta.
Za ki samu ganyen gwanda ki wanke da ruwan dumi da gishiri amma ba wai dirjewa fa za ki yi ba sama sama saboda dattin dake jikin gayen da sauran cutuka su fita. Sai ki samo tsamiya, citta, tafarnuwa da gishiri.
Ki samu ruwa ki zuba kamar lita goma 10 ki tabbata 10 din ne sai ki saka ganyen gwanda, tsamiyya, citta, da tafarnuwarki a ciki sannan ki zuba gishiri babban cokali biyu 2 ki dora a wuta ki tafasa shi sosai da sosai kina shan ruwan safe da dare in sha Allahu duk wani abu da ya danganci ciwon Sanyi (infection) namu na mata da duk wani abu da ya danganci irin wannan matsalar zai wanke shi da yardar Allah.
Allah ya sa mu dace.