Gwamnatin jihar Kogi ta ayyana ranar Alhamis 29 ga watan Disamba, 2022 a matsayin ranar hutu a shirin jihar na karbar bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari a wannan rana domin kaddamar da ayyukan da gwamna Yahaya Bello ya gudanar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kingsley Fanwo ya raba wa manema labarai a Lokoja a ranar Lahadi.
Gwamnatin jihar ta bukaci al’ummar jihar Kogi da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tarbar shugaban kasar da kuma nuna karamcin da aka sansu da shi a jihar.
Kazalika, gwamnatin jihar ta bukaci dukkanin kungiyoyin kwadago da hukumomin tsaro da su tabbatar da cikakken bin umarni don tabbatar da cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar jihar cikin aminci.