Jami’an ‘yansanda sun kama wasu mutane shida da ake zargi da sace wani Ojo Tobi David, dalibi a jami’ar Sa’adu Zungur, Gadau a jihar Bauchi da ke matakin 400, biyo bayan rashin fahimtar juna tsakaninsu game da raba dala 3,800 da suka samu ta hanyar zamba a yanar gizo.
LEADERSHIP ta tattaro cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, Damilola James, ya yanke jiki ya fadi ya mutu yayin da yake kokarin tsere wa jami’an soji na musamman ta bataliya 133 da ke Azare yayin da suka farmaki wadanda ake zargin, sojojin sun mika wadanda ake zargin ga jami’an ‘yansanda.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, (PPRO), SP Ahmed Mohammed Wakil, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba ya ce, biyu daga cikin mutane shidan da aka kama sun hada da daliban jami’ar Sa’adu Zungur a mataki 300 da mataki 400, su ne Abdulkarim Gobir da Ibrahim Yusuf.
Sauran wadanda ake zargin da suka shiga hannun jami’an ‘yansandan sun hada da Hassan Mohammed, Peter Femi da Samuel Abimbola.