Kamfanin samar da wutar lantarki na kasa (TCN), ya ce kungiyar kwadago ta rufe tashoshin samar da wuta ta kasa, lamarin da ya haifar da rashin wutar a fadin Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da TCN ta fitar, ta bayyana cewa, an rufe tashar ne da misalin karfe 2:19 na daren washe garin Litinin, 3 ga Yuni, 2024.
- Gwamna Yusuf Zai Ayyana Dokar Ta-ɓaci A Fannin Ilimi A Kano
- Gobe Za a Tsunduma Yajin Aiki, An Gaza Cimma matsaya Tsakanin Gwamnati Da NLC
Rufe tashoshin an fara ne daga tashar Benin zuwa wasu tashoshi a Ganmo, Benin, Ayede, Olorunsogo, Akangba da Osogbo.
Da misalin karfe 3:23 na safiyar litinin, TCN ta ce ta fara aikin mayar da wutar, ta hanyar amfani da tashar Shiroro don karfafa layukan wutar lantarki zuwa ga tashar Katampe.
TCN ta ba da tabbacin cewa, za ta ci gaba da kokarin farfadowa da daidaita wutar lantarki don tabbatar da maido da wutar zuwa cibiyoyin rarraba wutar a fadin kasar.