Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU reshen jihar Kaduna (KASU) ta ki komawa bakin aiki duk da barazanar da gwamna Nasir El-Rufai ya yi na korar su.
Hukumar kula da makarantar ta bukaci daliban da su koma karatu domin yin jarrabawar su bayan barazanar da gwamnan ya yi.
A ranar Litinin din da ta gabata, an ga wasu daga cikin daliban KASU suna rubuta jarabawarsu karkashin kulawar mataimakin shugaban jami’ar da sauran ma’aikatan cibiyar.
Daily trust ta nakalto cewa ‘ya’yan kungiyar ASUU reshen Jami’ar Kaduna (KASU) sun ki shiga aikin kula da daliban masu jarrabawa, inda suka yi ikirarin cewa har yanzun suna cikin yajin aiki.
ASUU-KASU a wata sanarwa da ta fitar a karshen taronta da ta gudanar a ranar Litinin ta ce, an samu kura-kurai a lokacin kula da jarrabawar.
Shugaban kungiyar ASUU-KASU reshen jihar da sakatarenta, Kwamared Peter Adamu da kwamared Usman Abbas ne suka sanya wa sanarwar hannu.