Mataimakin sakataren kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiyar kasar Sin, kuma mataimakin daraktan hukumar sa ido ta kasa Xiao Pei, ya bayyana a yau Litinin cewa, yaki da cin hanci da rashawa na iya ci gaba ne kawai, ba zai ja da baya ba, kuma dole ne a yi nasara da gaske a yakin da ake da cin hanci da rashawa, da kyautata tsarin hana yaduwar cin hanci da rashawa, da samun karin nasarori a hukumomi, da karfafa amfanin gudanarwa a fannin.
Xiao ya bayyana haka ne, a yayin taron manema labaru da aka shirya a wannan rana, a cibiyar watsa labaru ta babban taron wakilan jam’iyyar JKS karo na 20.
Ya kara bayyana cewa, bisa sakamakon wani binciken jin ra’ayin jama’a da kwamitin ladabtarwa na tsakiya, da hukumar kididdiga ta kasa suka gudanar a wannan shekarar, an ce, kashi 97.4% na al’ummar kasar sun yi imanin cewa, gudanarwa, da matakai masu tsanani da jam’iyyar JKS ke aiwatarwa na da amfani, adadin ya karu da kashi 22.4% bisa na shekarar 2012.
Kaza lika kashi 99% na jama’ar kasar sun yi imanin cewa, matakan da kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ya dauka, na tabbatar da da’a da yaki da cin hanci da rashawa, sun nuna cikakken ruhin jam’iyyar na neman sauye-sauye. (Mai fassara: Bilkisu Xin)