Mashawarciya ta musamman kan harkokin lafiya ga Gwamnan Jihar Kano, Dakta Fauziyya Buba Idris ta bayyana cewa kyakkyawan shirin da aka bijiro da shi domin dakile matsalar dutar kwakwalwa da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin daliban makarantun gaba da sakandire kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.
Mashawardiya kuma shugabar kwamitodi magande matsalar kwakwalwa da kwamitin yaki da sha da fataudin miyagun kwayoyi ta bayyana haka yayin taron da aka gudanar da malaman makarantun gaba da sakandire a Jihar Kano.
- Zan Magance Rashin Aikin Yin Matasa Da Dala Biliyan 10 – Atiku
- Matsalar Karancin Man Fetur Na Ci Gaba Da Ta’azzara A Legas
Dakta Fauziyya ta de an shirya taron ne domin dubawa tare da nazarin shawarwarin da aka zartar a taron da ya gabata domin yin nazari don ganin shin ko malaman sun aiwatar da wadannan shawarwari? kuma alhamdulillahi, an tabbatar da fara aiwatar da wadandan shawarwari, domin zuwa yanzu har an kafa kulib-kulob na yaki da shaye-shayen da matsalar kwakwalwa a wasu makarantun gaba sakandire a Jihar Kano.
Mashawardiyar ta di gaba da cewa zuwa karshen wannan watan, kwamitodin da aka kafa za su fara zagayen makarantun gaba da sakandire domin ganin irin di gaban da aka samu.
Dakta Fauziyya ta jadadda bukatar da ake da ita ga malaman domin kara himma wajen sa ido kan dalibansu, kamar yadda su ma daliban aka fadakar da su yadda za su lura da lafiyarsu ba kawai tsaftar jiki ba. Don haka sai ta tabbatar da aniyar wannan gwamnati na ganin matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi sun zama tarihi nan ba da jimawa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp