Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta shawarci ‘yan Nijeriya da su fice daga kasar Lebanon biyo bayan hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai wa kungiyar Hizbullah da wasu yankunan kasar Lebanon.
Hukumar ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM) ce ta ba da wannan shawarar a ranar Laraba a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta, Abdur-Rahman Balogun ya sanya wa hannu.
- Tinubu Zai Yi Balaguro Zuwa Birtaniya Na Mako 2
- Jirgin Ruwa Dauke Da ‘Yan Maulidi 200 Ya Nutse A Neja
Sanarwar ta ce, duk da cewa, rahotonnin sun tabbatar da cewa, al’ummar Nijeriya mazauna kasar Lebanon da yawansu sun yi kaura daga kudancin kasar kuma suna cikin koshin lafiya, amma “muna ba su shawara da su zama cikin kula har zuwa lokacin da za a tsagaita bude wuta a tsakanin bangarorin biyu”.
Gwamnatin ta bayyana jin dadin ta cewa, babu wani dan Nijeriya da harin ya rutsa da shi.
A ‘yan kwanakin da suka gabata, hare-haren da jiragen yakin Isra’ila ke kai wa kasar Lebanon sun kara tsananta, inda suka kai hari kan wuraren da kungiyar Hizbullah ta ke a Beirut da kuma kudancin Lebanon.
Hare-haren ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 600, ciki har da shugaban kungiyar Hizbullah, Hassan Nasrallah, tare da raba dubunnan mutane da muhallansu.