Amurkawa na kara damuwa game da yakin haraji da gwamnatinsu ke gudanarwa a sabon zagaye albarkacin kusantowar kafuwar sabuwar gwamnatin kasar. A watan Disamba na shekarar bara, wani bincike da aka yi, bisa jin ra’ayin Amurkawa 2000, sulusinsu na cike da matukar tsoro, da damuwa game da manufar harajin da sabuwar gwamnatin kasar za ta aiwatar a nan gaba.
Yawan sayayya fiye da kima, da adana hajoji a cikin gida da Amurkawa suke yi bai zo da mamaki ba, duba da cewa, bisa wasu binciken da aka yi, matsin lamba da batun haraji ke haifarwa na damun Amurkawa masu sayayya. Kazalika kara buga haraji kan hajojin dake shiga kasar ya haifar da hauhawar farashi da ya kai kaso 10% a wani lokaci.
- Xi Ya Zanta Da Babban Jagoran Vietnam Da Shugaban Sri Lanka
- Hauhawar Farashin Kayayyaki Ya Kai Kashi 34.80 A Disamban 2024 – NBS
Daya daga cikin dalilan da gwamnatin Amurka ke cewa ya sa ta aiwatar da manufar harajin shi ne burin dawo da masana’antun samar da kayayyaki cikin gida. To sai dai kuma sakamakon da aka samu ya saba da hakan. Zai fi kyau a yi tunani mai zurfi kan matsalolin da tattalin arzikin Amurka ke fuskanta, a maimakon raya masana’antar samar da kayayyaki ta hanyar aiwatar da manufar haraji.
Bari mu duba bangaren samar da guraben aikin yi. Wannan manufa ta ba da kariya ga wasu sana’o’i, amma a daya hannun, matakin da wasu kasashe suka dauka na martani, ya haifar da raguwar ribar kamfanonin Amurka, da ma tsagaita ajandar karuwar albashi, da shirin habakar kamfanonin kasar, da ma illata halin samar da guraben aikin yi.
Gwamnatin Amurka na amfani da haraji wajen cimma burinta na siyasa, amma matakin ba zai hana bunkasuwar Sin ba ko kadan, kuma ba zai haifar da jinkirin zuba jarin kamfanonin kasar a kasar Sin ba.
Gwamnatin Sin ta fitar da alkaluma dake cewa, a shekarar bara, yawan hajojin da Sin ta yi shige da ficensu ya kai sabon matsayi a tarihi, yayin da cinikin shige da fice na Sin ya kai matsayin farko a duniya a cikin shekaru 8 a jere. Har illa yau, Amurkawa sun kafa kamfanoni fiye da dubu 73 a Sin, kana yawan kudin da suka zuba a Sin ya kai fiye da dala triliyan 1.2.
Cimma nasarori tare tsakanin bangaren Sin da Amurka, zarafi ne ga saura a maimakon kalubale, don haka ya kamata sun yi hakuri da juna, su samu ci gaba da wadata irin nasu, domin kaucewa dandana bacin rai sakamakon yakin haraji da ciniki. (Amina Xu)