Kungiyar ‘yan kwadago a jihar Neja ta sanar da tsunduma yajin aikin sai-baba-ta-gani wanda zai fara aiki daga ranar Laraba 21 ga Fabrairu, 2024.
Kungiyar ta ce, acikin wata wasika da ta aikewa gwamnatin jihar Neja ta ofishin sakataren gwamnatin jihar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar NLC na jihar Idris A. Lafene da shugaban kungiyar TUC na jihar Ibrahim Gana, matakin zai dore har sai gwamnati ta warware duk wata takaddamar da ke tsakaninta da su.
- Sake Zaben Cike Gurbi: ‘Yansanda A Kano Sun Gargadi Magoya Bayan APC Da NNPP Kan Tarzoma
- Kwastam Za Ta Raraba Wa ‘Yan Nijeriya Shinkafa Da Sauran Kayan Da Ta Kwato
Kungiyar ta bukaci gwamnatin jihar da ta sauya duk wasu nade-naden siyasa da ta yi akan kujerar manyan daraktocin kudi, ayyuka da gudanarwa a hukumomi.
Haka kuma, ta bukaci gwamnati da ta sauya nadin shugabanni da mambobi na dindindin da kwamishinonin na hukumar ma’aikatan kananan hukumomi da kuma nadin manyan daraktoci na wasu hukumomi.
Sauran bukatu sun hada da “bukatar gwamnati ta bayyana karara kan karin biyan albashin ma’aikata.”
Kungiyar kwadagon ta kuma gargadi gwamnatin jihar da ta daina cin zarafin malamai biyo bayan muhawarar makarantar firamare da aka yi a garin Agaie da gwamnatin ta yi zargin wani dalibi da yin amfani da kalaman batanci da kiran yin bore ga gwamnatin tarayya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp