Shugaban majalisar dattawa, Godswill Obot Akpabio, ya bayyana cewa wasu ‘yan siyasa daga jihohin Adamawa da Kwara da ke jam’iyyun adawa na kitsa makarkashiyar tsige shi daga mukaminsa.
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya amshi bakoncin shugabannin kungiyoyin matasan Neja Dalta a Abuja.
- Mutane 7 Sun Mutu, Kadarorin Miliyan 50.3 Sun Salwanta Dalilin Gobara A Kano
- Wata Rana Za A Yi Wa Gwamnatin Tinubu Sambarka – Minista
Ko da yake bai ambaci sunaye ba, amma maganar ta yi nuni ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki wadanda suka fito daga Adamawa da Kwara, kuma a kwanakin baya ne suka fitar da sanarwar ya sauka daga shugabancin majalisar dattawa sakamakon lamarin da ya janyo cece-kuce tsakaninsa da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Duk da sun san cewa dokokin majalisar dattawan da suka shafi rashin da’a, Akpabio ya koka da cewa mutanen da ake magana da su suna yin watsi da hakikanin al’amuran da gangan saboda siyasar adawa.
“Don haka lokacin da mutane suka hada kai, sai na ji muryoyi daga Adamawa da Kwara suna ihu,ana amfani da wasu matasa daga yankin kudu maso yamma wajen yin adawa ta siyasa.Ya kamata mutum ya dunga tauna magana kafin ya fade ta”, n ji shi.
Da yake jaddada cewa ya kamata mutane su fahimci cewa a matsayinsa na shugaban majalisar dattawa, ba wai shi kadai ke wakiltar mazabarsa da jam’iyyarsa ba, har ma da yankin da ba a taba rike wannan mukami ba tsawon shekaru 46 da suka gabata.Shugaban majalisar ya bukaci wadanda ke sukar sa da su yi shiru da bakinsu.
Akpabio ya bayyana cewa shugaban majalisar dattawa ba wai kansa kadai yake wakiltar ba, al’ummar yankin Neja Delta gaba daya ba yake wakilta.
A yayin da yake jawabi a kan batun samar da kujerun zama da ya shafi Natasha Akpoti-Oduaghan, wanda ya kai ga zargin cin zarafi, Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa mutane suna ihu ne kawai ba tare da fahimtar ka’idojin da aka shimfida ba na majalisar dattawa.
Ya ce wadanda ba su san ayyukan cikin gida na majalisar dokoki ta kasa ba za su iya fahimtar abin da ya kai ga dakatar da Natasha ba.
Da yake kare matakin dakatarwar da aka yi wa Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida, Akpabio ya bayyana cewa, matakin bai daya ne na daukacin majalisar ba tare da ko daya daga cikin ‘yan majalisa da ya nuna adawa da shi ba.
Shugaban majalisar ya bukace masu sukar da su daina yin sharhin da ba su sani ba game da majalisar.
Tun da farko, Shugaban Majalisar Matasan Ijaw,Jonathan Lokpobiri wanda ya jagoranci tawagar ya nuna damuwarsa game da abubuwan da ke faruwa a majalisar dattawa, ya kuma tabbatar wa Akpabio cewa mutanen Neja Delta suna mara masa baya.
Lokpobiri ya kuma nemi shugaban majalisar dattawan ya sa baki kan rikicin da ke kunno kai a Jihar Ribas, yana mai gargadin cewa za ta iya nausawa har zuwa yankin Neja Delta baki daya idan ba a yi la’akari da shi ba.
Game da yanayin da ya shafi Natasha, shugaban matasan ya nuna damuwarsu, ko da ya ce ya kamata a dauki lamarin a matsayin batun cikin gida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp