‘Yan bijilante ta sun kama wasu mutane hudu bisa zarginsu da kashe wani tare da kone gawar mutumin a garin Benin da ke Jihar Edo.
Majiyarmu ta ce an gano gawar ne a cikin harabar tsohon dakin kwanan dalibai da ke Kwalejin Jinya na Asibitin Kwararru da ke birnin Benin.
- Bayan Kayan Angonci Sun Yi Batar Dabo, An Sace Sadakin Amarya A Taron Daurin Aure
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutane A Masallaci A Delta
Kodinetan ‘yan bijilante a jihar, Kanal Kole Oshoriamhe Omomia, ne ya shaida hakan a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a birnin Benin a ranar Juma’a.
Omomia ya ce, “Jami’anmu suna kan sintiri kamar yadda suka saba sai suka samu bayanin cewa akwai wani mutum tsaye a cikin wani gini kuma akwai gawa a kwance a inda yake.
Lokacin da mutanenmu suka isa wajen, sun tarar da gawar a kone.”
Ya ce, an sun kama mutum hudu da suke zargi kuma tuni suka mika su ga ‘yansanda domin zurfafa bincike.
Ya kara da cewa babban wanda ake zargi mai suna Nwafor Azubuike, an samo shi a wannan ginin da aka gano gawar a ciki.
“Nwafor Azubuike wanda ya yi ikirarin cewa na zaune a wajen, ya ce ya san mamacin kuma kwanakin da suka gabata ma har sun yi magana.
“Kallon ginin ma shi kansa, mun yi amannar cewa a nan ana gudanar da ayyukan ta’addanci. Mun kuma gano gashin mutane da dama a yankin, kamar gashin mata ne,” ya shaida.