Ministan Wutar Lantarki, Adelabu, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su nuna kishin kasa a duk lamuransu musamman kan kadarorin kasa.
Adelabu ya yi wannan kiran ne a sakonsa na sabuwar shekara ta wata sanarwa da Bolaji Tunji, mashawarcinsa na musamman kan harkokin sadarwa da hulda da manema labarai ya fitar.
- Gwamnatin Tarayya Ta Rabar Da Naira Biliyan 16.1 Ga Masana’antu 22 — Ministan Kudi
- Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Masu Shirin Tafiya Zuwa Australia
Ya nuna matukar damuwarsa kan yadda ake yawan kai hare-hare da barnata turakun wutar lantarki. Ya danganta harin da ake kai wa akai-akai, wanda ya ce ya yi illa ga karuwar samar da wutar lantarki ga gidaje da ‘yan kasuwa.
A cewarsa, babban abin da ya kawo cikas ga samun nasarar samar da wutar lantarki a kasar nan a shekarar da ta gabata, shi ne, hannun wasu ‘yan Nijeriya marasa kishin kasa ne wadanda suka bayyana a matsayin ‘yan bindiga.