Rundunar ‘yan Sanda a jihar Katsina ta tabbatar da farmakin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka yi shigar Burtu inda suka sanyi Abaya sannan suka kai hari ga wani shingen jami’an tsaron haɗin gwiwar tsaro kuma sun kashe mutum biyu.
Kakakin rundunar ‘yan Sanda a jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ƙara da cewa tuni an tura jami’an tsaro domin kamo waɗanda suka yi wannan ta’asa.
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Mutane 29 A Kauyen Katsina
- ‘Yan Bindiga Sanye Da Hijabi Sun Farmaki Ofishin ‘Yansanda A Katsina
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi shigar ɓadda bani ne inda suka farmaki shingen jami’an tsaro da ke kauyen gurbin magarya akan hanyar Batsari zuwa jibiya a jihar Katsina
Shaidun gani da ido sun tabbatarwa Leadership Hausa cewa an kai wannan harin ne a ranar Alhamis da yamma wajen misalin karfe huɗu da marece a kauyen gurbin magarya
A cewar mai bada labarin ‘yan bindiga sun zo ne akan mashina sannan sun yi nasarar kashe ‘yan Sanda guda 2 masu muƙamin insifakta sannan sun guda da bindigogin su, suka bar motar sintirin jami’an tsaron a wajan.
Wata majiya ta shaidawa Leadership Hausa cewa tuni aka ɗauke gawarwakin ‘yan sandan da aka kashe zuwa babar asibitin Katsina.
Idan za a yi tunawa wannan yanki na Batsari da Jibia na fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da sace jama’a domin biyan kudin fansa duk da ƙoƙarin da gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ke cewa suna yi domin shawo kan matsalar tsaro.