Wasu ‘yan bindigan da ba a gano ko su waye ba zuwa yanzu sun kai hari gidan babban mai taimaka wa gwamnan Jihar Bauchi kan harkokin kula da Kiristoci, Fasto Zakka Luka Magaji a gidansa da ke kauyen Birshi da ke cikin garin Bauchi.
‘Yan bindigan da yawansu ya kai bakwai sun mamaye gidan Luka ne da kokarin yin garkuwa da shi ko barazana ga rayuwarsa. Amma cikin ikon Allah basu samu nasarar hakan ba
- Kamfanonin Kasar Sin Sun Shirya Taron Horar Da Matasan Afrika
- Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Zarce Yadda Ake Tsammani
A lokacin harin, wani matashi mai shekara 32 da ya kasance mambar cocin Christian Life da ke zaune tare da Fasto Zakka din an jikkata shi.
A lokacin da kwamishinan kula da harkokin addinai na jihar Bauchi, Hon Umar Babayo Kesa ya jagoranci tawagar ma’aikatarsa don kai ziyarar jaje ga Faston, Zakka ya shaida cewa ba su san dalilin wadanda suka kawo masa harin ba, “Amma cikin ikon Allah, Allah ya karemu. Kuma wadda ya jikkatan zuwa yanzu yana samun sauki.”
A nasa fannin, Umar Babayo Kesa, ya shaida cewar sun zo ne domin jajanta wa Faston bisa wannan harin da aka kai masa.
Ya yi addu’ar Allah ya cigaba kare shi da iyalansa daga hannun miyagun.
Faston ya gode musu bisa wannan ziyarar ya nuna hakan a matsayin matakin da zai Kara kyautata zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar.
Ita ma rundunar ‘yansandan jihar Bauchi, ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakinta, Ahmed Wakil, inda ya ce tunin aka fara kokarin cafko maharan.
Ya ce, rundunar ta samu kiran waya kan lamarin wajajen karfe 0013hrs inda suka dauki matakin tura jami’ai da kai daukin gaggawa.
Ya ce lokacin da jami’an ‘yansandan suka isa wajen, sun samu kwanson harsasai uku samfurin 7.6mm.
Wakil ya kara da cewa sun dauki wadda aka jikkata zuwa asibitin ATBUTH domin kulawar Likitoci
Ya cigaba da cewa suna kokarin daukan matakan da suka dace domin cafko wadanda suka kai wannan harin.