‘Yan sanda uku ne ake fargabar an kashe su a ranar Asabar a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a shingen binciken su da ke Agbani, hedikwatar karamar hukumar Nkanu ta Yamma a jihar Enugu.
Wasu da dama kuma sun jikkata yayin harin, wanda ya faru a wani shataletale da ke kusa da ofishin ‘yan sanda na yankin Agbani.
Jami’an ‘yan sandan na cikin aikin bincike ne lokacin da maharan suka hango su, nan take suka bude musu wuta, inda suka harbe jami’an uku.
‘Yan bindigar na cikin wata mota ne yayin da aka rahoto cewa sun yi nasarar tsere wa ta hanyar zuwa Ugbawka.
Harin dai ya faru ne kasa da sa’o’i 24 bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe tsohon kwamishinan jihar kuma tsohon shugaban karamar hukumar Oji-River, Cif Gabriel Onuzulike da kuma dan uwansa a garinsu na Nkpokolo-Achi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp