Wasu ‘yan bindiga sun kai hari babban asibitin karamar hukumar Kankara a jihar Katsina, inda suka harbi wani likita tare da yin garkuwa da wasu ma’aikatan jinya da ba a tantance adadinsu ba.
Harin ya faru ne da misalin karfe 7:00 na daren ranar Talata, inda suka harbi Dakta Murtala Sale Dandashire.
- Hamas Ta Amince Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Da Isra’ila
- Afrika Na Da Damar Kawowa Kanta Ci Gaba – Tinubu
A cewar wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ‘yan bindigar sun mamaye harabar asibitin ne a wani harin da suka kai musu, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin ma’aikatan da marasa lafiya inda suka yi ta harbe-harbe ba kakkautawa.
Mazaunin garin ya tabbatar da cewa, Likitan da aka harba a kafarsa, a halin yanzu yana raye kuma yana karbar magani a wani asibiti da ba a bayyana ba.
Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Katsina, Sadiq Abubakar, ya tabbatar da faruwar harin, inda ya tabbatar wa wakilinmu cewa, zai yi karin bayani kan abin da ya faru yayin da rundunar ‘yansandan ke ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.