Wasu dauke da muggan makamai da ake kyautata zagon masu garkuwa da mutane ne sun kai hari zuwa gidan tsohon ministan yada labarai, Labaran Maku da ke yankin Ola a karamar hukumar Akwanga da ke jihar Nasarawa.
Uku daga cikin jami’an tsaron da suke aikin bada tsaro a gidan sun gamu da munanan raunuka a sakamakon harin da ‘yan bindigan suka kai a ranar Asabar.
A cewar daya daga cikin masu tsaron, maharan sun yi ta kokarin kutsa kai zuwa cikin gidan amma sun gamu da tirjiya daga masu tsaron gidan.
“Lokacin da suka tabbatar ba za su iya shiga gidan ba, sai suka fara harbin kan mai uwa da wabi,” ya shaida.
Daga bisani lokacin da suka ji duriyar karin jami’an tsaro da suka kawo dauki daga Akwanga, ‘yan bindigan sun arci na kare.
Tsohon Ministan, Labaran Maku wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi ya ce wannan shi ne irinsa na uku da ya faru cikin wata daya.
Ya ce, jami’an tsaron soji da ‘yansanda ne suka taimaka wajen gaggawar kai dauki zuwa gidansa domin fatattakar ‘yan bindigan.
“Idan za ku tuna sun mamayi gidan Babana da ke Wakana suka yi garkuwa da ‘yan uwana uku a watan da ya gabata. A wani lokaci kuma sun kashe ‘ya’yan yayana uku. Wannan lamarin na nuni da cewa jiharmu kawai tana mamaye ne da ‘yan bindiga.”
Kazalika, gwamnan Jihar, Abdullahi Sule, ya yi Allah wadai da harin da aka kai zuwa gidan tsohon ministan.
A sanarwar da mai dafa masa kan harkokin hulda da jama’a, Mr Peter Ahemba a ranar Lahadi cikin wata sanarwa ya misalta harin a matsayin mummunar lamarin da ba za su lamunta ba.
Ya ce tunin gwamnan ya umarci jami’an tsaro da su farauto maharan tare da tabbatar da gurfanar da su.
Ya ce, gwamnatinsa ta himmatu wajen kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar. Daga bisani ya jajanta wa tsohon ministan bisa wannan lamarin.