Akalla mutane 40 ne aka yi garkuwa da su a wani masallaci da ke kauyen Gidan Turbe a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara a safiyar ranar Litinin.
Hakan ya nuna koma baya ga yarjejeniyar zaman lafiya a jihohin Katsina da Zamfara da aka yi da ‘yan bindigar da ke addabar yankin Arewa maso Yamma.
- Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
- KEDCO Ta Mayar Da Wutar Lantarki A Asibitin Aminu Kano
Daily Trust ta ruwaito cewa, shugabannin al’umma da ‘yan bindiga a karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, a ranar 28 ga Agusta, 2025 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya.
Yarjejeniyar, a cewar daukacin mahalarta taron, ta nuna wani gagarumin mataki na kawo karshen tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane da satar shanu a Arewa maso Yamma, da kuma yankin Arewa.
Yarjejeniyar wacce Mai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi, da shugaban karamar hukumar, Babangida Abdullahi Kurfi suka shirya, ta gudana ne a dajin Wurma, inda ake fama da rashin tsaro.
Manyan jagororin ‘yan bindigan da suka hada da Alhaji Usman Kachalla Ruga da Sani Muhindinge da Yahaya Sani (Hayyu) da kuma Alhaji Shu’aibu duk sun yi alkawarin tsagaita wuta.
Daga baya suka sako mutanen da suka kama kuma suka bar manoma su koma gonakansu ba tare da wata barazana ba.
Sai dai kasa da wata guda da kulla yarjejeniyar, an tattaro cewa ‘yan bindigar sun sake kai hari a Zamfara inda suka yi awon gaba da masallata da dama.
Wata majiya ta cikin garin, ta shaida cewa, harin ya afku ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5:30 na safe, inda ‘yan bindigar suka afkawa masallacin, suka kewaye shi, sannan suka tattara masallatan zuwa daji.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp