Aƙalla sojoji biyu sun samu raunuka yayin wani hari da ‘yan ta’adda suka kai sansanin sojoji da ke Tegina, a karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja.
Har ila yau, an tabbatar da kashe ɗaya daga cikin ‘yan bindigar a fafatawar tsakaninsu da sojojin.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji A Kan Hanyar Abuja Zuwa Nasarawa
- Jirgin Sama Dauke Da Mataimakin Shugaban Kasar Malawi Ya Yi Batan-Dabo
Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar na kokarin tsallakawa zuwa wasu kananan hukumomin jihar ne, yayin da suka kaddamar da harin a sansanin sojoji.