Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kewaye masallata a ƙaramar hukumar Ƙanƙara ta jihar Katsina a ranar Alhamis, inda suke halaka mutane uku tare da yin garkuwa da wasu da dama.
Kamar yadda wata majiya ta bayyana, ta ce maharan sun shammaci masallatan ne inda suka buɗe musu wuta a daidai lokacin da suke gabatar da Sallar Isha’i, kuma nan take mutane uku suka rasu, sannan suka sace wasu da dama.
- Hukumar Zaɓe Ta Jihar Katsina Ta Ayyana Ranar Gudanar Da Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Jihar
- Ɗan Majalisa Ya Ɗauki Nauyin Kudin Makarantar Ɗalibai 60 A Katsina
Majiyar ta ci gaba da cewa ‘yan bindigar sun ƙara kutsa-kai cikin gari inda suka yi garkuwa da miji da mata, sai dai kash! sun kashe mijin saboda kin yarda da ya yi su tafi da shi.
“Abin baƙin ciki shi ne yadda wannan magidancin ya rasa ransa saboda jayayya da turjiya da ya nunawa maharan wanda kuma hakan ya yi sanadiyar tafiyarsa gidan gaskiya” inji majiyar
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, a cikin wannan dare ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan wani Ɗan banga mai suna, Sani maikifi a unguwar Tudun Boka cikin garin Ƙanƙara, sai dai shi ya yi nasarar tsallake rijiya da baya, amma sun yi awon gaba da ɗansa da kuma matarsa.
A cewar rahotanni tuni ‘yan bindiga ke fakon Sani maikifi wanda ake kyautata zaton cewa hakan ne dalilin kai wannan farmaki a garin ƙanƙara.
Sai dai kuma a daidai lokacin haɗa wannan rahoto gwamnatin jihar Katsina da kuma rundunar ‘yan sandan jihar babu wanda ya ce uffan game da wannan harin wuce gona da iri.
Kazalika waɗannan hare haren na ci gaba da wakana a daidai lokacin da jami’an tsaro ke kokarin ganin an kawo karshen wannan lamari da yunkurin gwamnatin jihar na samar da dakarun tsaro na ‘Community Watch Corps”