‘Yan bindiga sun yi wa mutane uku kwanton ɓauna inda suka harbe su a karamar hukumar Doma ta jihar Nasarawa.
Wadanda lamarin ya rutsa da su sun hada da Tailor Gayu, wanda aka fi sani da Reverend Father, Zacharia Wudu, da James Delle Iwala.
ADVERTISEMENT
Wannan lamari ya faru ne kwana biyu bayan da Gwamna Abdullahi Sule ya yi alƙawarin murkushe masu aikata laifuka da ke kutsawa cikin jihar don kawo cikas ga zaman lafiya.
LEADERSHIP ta rahoto cewa, ‘yan bindiga sun kai hari a ranar Juma’ar da ta gabata a garin Sarkin Noma da ke karamar hukumar Keana a jihar, inda suka kashe mutane biyu sannan suka yi garkuwa da wani dattijo.














