Akalla mutum 37 ne rahotanni suka tabbatar da ‘Yan bindiga sun kashe a wasu sabbin hare-hare da suka kaddamar a karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.
An kaddamar da hare-haren a wurare daban-daban a daren Lahadi a kauyukan Malagum 1 da Sokwong na masarautar Kagoro a karamar hukumar Kaura ta jihar.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Dakile Hari A Kaduna
- ‘Yan Bindiga Sun Harbe Shugabar Matan Jam’iyyar LP A Jihar Kaduna
Duk da cewa hukumar ‘Yan sandan Jihar ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba.
Shugaban Karamar Hukumar Kauru, Hon Atuk Stephen, ya shaida wa gidan Talabijin na Channels ce wa ‘Yan bindigar sun kai harin ne a daidai lokacin da misalin karfe 11 na daren ranar Lahadi inda suka suka kashe mutane 37.
Ya kuma ce ‘Yan bindigar sun kona gidaje sama da 100 tare da lalata motoci da babura da dama a yayin harin.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun lalata dukkan gidajen da ke yankin Sokwong gaba daya, yayin da yankin ya zama ba kowa.