Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kisan mutane shida da yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a karamar hukumar Faskari ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO, ASP Abubakar Aliyu), ya tabbatar da kisan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 6, Sun Sace 38 Tare Da Ƙone Dukiyoyi A Katsina
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Masallata Uku Da Sace Mutane Da Dama A Katsina
Ya ce an kuma jikkata mutane 10 a harin wanda ya faru a kauyen Nasarawa ranar Lahadi.
“A ranar 19 ga watan Fabrairu da misalin karfe 11:30 na rana wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da yawansu dauke da muggan makamai irin su AK-47, sun kai hari kauyen Nasarawa da ke karamar hukumar Faskari.
“Sun harbe mutane shida, sun raunata 10, sun kona gidaje uku da motoci kusan 10,” inji shi.
Abubakar ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Aliyu Musa, ya tura jami’an tsaro da kuma jami’an leken asiri zuwa wurin.
Ya ce jami’an ‘yan sandan na sintiri a dazukan domin samun nasarar cafke wadanda suka aikata wannan aika-aika