‘Yan bindiga sun kara kai wani hari a wajen duba ababen hawa a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, inda suka hallaka ‘yan sintiri shida.
Lamarin wanda ya afku a jiya Talata, daya daga cikin ‘yan sintirin mai suna
Usman Babangida a yau Laraba ya ce, maharan sun kawo harin ne da misalin karfe 4:00 na yammar ranar Talata.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Muhammad Jalige bai fitar da wata sanarwar kan afkuwar lamarin ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp