Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da daliban wata Tsangaya da ba a san adadinsu ba a Gidan Bakuso da ke karamar hukumar Gada a jihar Sokoto a ranar Asabar.
Rahotonni na cewa an sace daliban ne daga makarantarsu da misalin karfe daya na daren ranar Asabar.
Shugaban makarantar, Liman Abubakar, ya shaida wa wakilinmu cewa dalibai 15 ne ba a ji duriyarsu ba amma har yanzu suna kan kirga adadin daliban.
Abubakar, ‘yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe daya na dare, inda suka harbe mutum daya sannan suka yi awon gaba da wata mata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp