‘Yan bindiga sun sace akalla mutane 44 a kauyen Kanwa da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun afkawa al’ummar yankin ne cikin dare, inda suka rika bi gida-gida suna yin garkuwa da mazauna yankin, galibinsu mata da kananan yara ne.
A baya-bayan nan, an samu kwanciyar hankali bayan an shafe shekaru ana kai munanan hare-hare a kan al’umomin kananan hukumomin, amma sace-sacen mutanen ya sake kunno kai, lamarin da ya sa mazauna garin suka koma zama cikin firgici.
Ana kyautata zaton wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga ne da ake kira Dankarami ne ya kai harin.
Daily Trust ta ruwaito yadda Dankarami yake ta addabar mazauna yankin Zurmi da Birnin Magaji da Jibia a jihar Zamfara da makwabciyar ta jihar Katsina.
Ya ce har yanzu ‘yan bindigar ba su kai ga kiran ‘yan uwan wadanda aka sace ba domin neman kudin fansa.
A halin da ake ciki, mazauna garin Moriki sun fara kokarin tattara “kudin kariya” bayan da ‘yan bindigar suka bukaci al’ummar da su ba su Naira miliyan 20 ko kuma su kawo musu hari.