Wasu mahara daba a san su waye ba sun yi awon gaba da Shugaban Karamar hukumar Akwanga da ke Jihar Nasarawa, Alhaji Safiyanu Isa Andaha da wasu abokan tafiyarsa.
Lamarin ya faru ne a ranar Littinin a kan hanyarsa ta zuwa kauyen Ningo da ke yankin Andaha.
- Hare-Hare: Gwamnatin Filato Ta Ayyana Zaman Makokin Mako Guda
- Shekarar 2024: Kyautata Fata A Cikin Duniyar Kalubale
Makusantan shugaban karamar hukumar sun tabbatar da faruwan lamarin ga manema labarai.
Sun tabbatar da maharan sun yi awon gaba da shugaban karamar hukumar a kan titin Akwanga zuwa Andaha, a ranar bikin sabuwar shekara da misalin karfe 8:30 na dare.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar Nasarawa, Mista Ramhan Nansel, ya tabbatar da faruwan lamarin.
Ya kuma ce rundunar ‘yansandan Jihar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kwato wadanda aka yi garkuwa da su da gaggawa ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp