Wasu ‘yan bindiga a ranar Asabar sun kashe akalla mutane 25 a wani hari da suka kai wasu kauyuka biyu a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Hare-haren sun zo ne mako guda bayan da ‘yan bindigar suka kashe fiye da mutane 25 da suka hada da ‘yan banga 16 a gundumar Kanoma da ke karamar hukumar Maru.
Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, wasu ‘yan bindiga sun mamaye kauyen Janbako kuma sun harbe sama da mutum 20.
“Sun isa kauyen ne a kan babura da misalin karfe 2 na rana, suka bude wa mazauna kauyen wuta.
“Bayan haka, ‘yan ta’addan dauke da makamai sun koma yankin Sakkida suka harbe mutum biyar a can,” inji Buhari Saminu mazaunin garin.
A halin da ake ciki, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana harin a matsayin dabbanci karara.
Ya ce, gwamnatinsa ba za ta nade hannunta ba, ta bar ‘yan ta’adda suna kashe al’umma ba gaira ba dalili ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp