‘Yan bindiga sun sako yara da ‘yan mata 74 da suka yi garkuwa da su a kwanakin baya sakamakon kisan da sojoji suka yi wa daya daga cikinsu a Wanzamai cikin karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Daya daga cikin iyayen yaran shi ne ya sanar da hakan ga wakilinmu a ranar Asabar, inda ya ce sun biya Naira miliyan shida a matsayin kudin fansa.
- Duk Da Kokarin Da Nijeriya Ke Yi Na Yakar Maleriya, Ita Ce Ta 32 A Yawan Mace-mace —Gwamanatin Tarayya
- Dabi’un Annabi (SAW) Na Cika Alkawari Da Mutunta Abokan Zama
Ya shaida cewar yara 74 da aka sako, suna daga cikin yara 99 da ‘yan bindigar suka sace, “Sun kashe biyu, daya ta gudu, sauran yara 22 ba mu san halin da suke ciki ba,” in ji daya daga cikin iyayen yaran da ya nemi a sakaya sunansa.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa mako uku da suka wuce ‘yan bindiga sun sace yara maza da mata 99 biyo bayan wani samamen da sojoji suka kai garin Wanzamai tare da kashe daya daga cikinsu.
‘Yan bindigar sun kashe yara biyu da nufin nuna fushinsu kan lamarin tare da sace yaran da cewa sai an biya Naira dubu ashirin kan kowane yaro kafin su sako su da kuma sharadin cewa sai an sauya Kwamandan sojin yankin.