‘Yan bindiga sun raba mazauna kauyuka a kalla 10 a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna da muhallansu sakamakon addabarsu da hare-hare da garkuwa da mutane.
Mafi yawan ‘yan kauyen sun yi kaura zuwa wasu garuruwan da ke karamar hukumar ne domin neman tsira da rayukansu, yayin da wasu kuma suka arci na kare zuwa karamar hukumar Zariya domin neman mafita.
- Likitocin Saudiyya Sun Yi Nasarar Raba ‘Yan Biyun Da Aka Haifa Manne Da Juna A Kano
- Bayan Wuya, Sai Dadi: Tinubu Ya Shaida Wa ‘Yan Nijeriya
Kamar yadda daya daga cikin shugabannin kauyukan da abun ya shafa, Malam Jafaru Anguwar Salahu, ke shaidawa cew, kauyukan da mafi yawansu manoma ne yanzu haka su na zama ne a wasu wuraren a matsayin ‘yan gudun hijira.
Ya jero kauyukan da abun ya shafa da suka hada da Sabon Gida, Anaba, Anguwar Salahu, Guberawa, Garu, Rafin Iwa, Gidanduki, Anguwan Najaja, Kunza, gami da Anguwan Magaji.
“Dukkanin wadannan kauyukan da na shaida akwai daruruwan mutane, amma a halin yanzu duk mun yi kaura mun bar gidajenmu da gonakanmu. Ya zuwa yanzu da muke magana, muna zaman gudun hijira ne a gundumar Gwada da wasu kauyuka.
“Muna rayuwa ne kawai, amma ba mu san me zai faru da mu ba,” ya shaida.
Malam Jafaru ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta zo ta kawo musu daukin gaggawa ta hanyar fatattakar ‘yan bindiga daga kauyukan nasu domin ba su damar komawa kauyukansu domin ci gaba da gudanar da harkokinsu na rayuwa ciki har da noma.