Sama da mutum hamsin ne aka bada labarin cewa ‘yan bindiga dadi sun kashe a kananan hukumomi biyu da suke jihar Sokoto a daren ranar Asabar.
Kananan hukumomin da lamarin ya faru a cikinsu su ne Gwadabawa da Tangaza dukka da suke jihar.
Kakakin hukumar ‘yansandan jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, ya bada tabbacin hukumar na kan binciken lamarin, kuma sun sha alwashin cewa za su sanar da ‘yan jarida karin bayanin da bincikensu ya nuna musu.
Sama da awanni da kaddamar da harin a yankuna uku da suke karamar hukumar Tangaza, gawarwaki 37 har yanzu ba a musu biso ba.
Yankunan da aka kai wa harin a daren ranar Asabar sun hada da Raka, Raka Dutse, da Filin Gawa da suke karamar hukumar Tangaza.
Tsohon shugaban karamar hukumar Tangaza, Bshar Kalenjeni ya tabbatar da cewa harin ya kashe18 a kauyen Raka, 17 kuma a Filin Gawa sai mutum biyu a Raka Dutse.
Wata majiya a Gwadabawa ta shaida ma wakilinmu cewa ‘yan bindigan sun kasance a yankin inda suka yi nazarin yadda za su kaddamar da harinsu ba tare da al’ummar garin sun sani ba.
“Sun hara kai harin ne bayan kammala sallar Isha’i inda suka kai wa shahararrun kauyuka biyu hari da Sakamaru da kauyen Bilingawa.
“A Bilingawa, sun kashe a kalla mutum 18, a Sakamaru Kuma abun ya kasanta domin yankan rago suka yi tabui wa mutane wasu kuma suka bindigesu. Sun yanka mutane kamar dabbobi suka Kuma konasu ta yadda ba ma a iya Gane waye wannan waye wancan,” ya shaida.