Wasu ‘yan bindiga dadi sun kai farmaki yankin Oko-Olowo da ke Illorin ta jihar Kwara da safiyar ranar Asabar, sun yi garkuwa da mutum uku.
Wadanda suka sace din sun hada da wani matashin Malamin addini, Alfa Sofiu Amolegbe, dan uwansa, Fasansi, gami da dansa mai suna Aliyu.
- Gobara Ta Kone Shaguna 15 Da Lalata Kaya Na Miliyan 19 A Jihar Kwara
- EFCC Ta Kama ‘Yan Damfara 18 A Jihar KwaraÂ
LEADERSHIP ta gano cewa ‘yan bindigar sun farmaki mutanen ne a gidansu da ke Oko-Olowo da ke kusa da babbar hanyar Ilorin zuwa Jebba inda suka kutsa kai ta cikin tagar gidan.
A lokacin da Fasansi ya yi kokarin arcewa daga hannun masu garkuwan sun ladabtar da shi da alburusai.
Mahaifin wadanda lamarin ya rutsa da shi, Imam Amolegbe da ke yankin Okelele, Ilorin, ya shaida wa jaridarmu cewa masu garkuwan sun watsar da Fansansi da tunaninsu na cewa ya mutu ne. Sai dai kuma ya tabbatar da cewa Fasansi a yanzu haka yana amsar kulawar Likitoci a wani wasi asibiti mai zaman kansa a Illorin.
Imam Amolegbe ya ce, daga bisani masu garkuwan sun tuntube su inda suka nemi kudin fansa na naira Miliyan 100 kafin su sake malamin da dansa, “sun nemi kudi har naira miliyan 100 a wajenmu, amma mun roke su da su karbi miliyan 10 saboda ba mu da kudi.